Datasets:
id
int64 0
57k
| text
stringlengths 252
23.2k
|
|---|---|
0
|
<|title|>Gwamna Yusuf ya bada tallafin Naira Miliyan 100 ga waɗanda gobara ta shafa a kasuwar Kantin Kwari
<|section|>news
Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya sanar da bayar da tallafin Naira Miliyan Dari ga wadanda gobara ta kone musu shaguna a shahararriyar kasuwar Kantin Kwari, a madadin gwamnatin jihar Kano. Gwamnan ya bayyana tallafin ne yayin da ya jagoranci wasu manyan jami’an gwamnati ziyarar ta’aziyya zuwa kasuwar a yau. A Sanarwar da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ta nakalto Gwamna Abba Kabir Yusuf yana mika jaje ga yan kasuwar da gobarar ta shafa. Gwamnan ya ce tallafin ba diyya ba ne ga asarar da aka yi, sai dai don rage radadin barnar da aka yi wa yan kasuwar da abin ya shafa. Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da shirin gwamnatin Kano na inganta yanayin kasuwanci a kasuwar ta hanyar girka fitilun hasken rana, gyaran hanyoyi, gina magudanun ruwa da kuma samar da rijiyoyin burtsatse da sauran su. Ya yi kira ga shugabannin kasuwar da su fara shirye-shiryen da za su taimaka wa dimbin yan kasuwar wajen gudanar da harkokinsu cikin sauki, tare da tabbatar da cewa gwamnatin jihar za ta yi duk mai yiwuwa don Kano ta ci gaba da zama cibiyar kasuwanci a Arewacin Najeriya da wasu kasashen Yammacin Afirka. Tun da farko, Manajan Darakta na Hukumar Gudanar da Kasuwar Kantin Kwari, Alhaji Hamisu Sa’ad Dogon Nama, ya bayyana cewa shaguna 29 ne gobarar ta kone, kuma ya gode wa jami’an hukumar kashe gobara da wasu da suka taimaka wajen dakile yaduwar gobarar. Shugaban kwamitin dattawan kasuwar, Alhaji Sabi’u Bako, ya gode wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan kulawarsa ga halin da yan kasuwar da abin ya shafa ke ciki, tare da rokon goyon bayan gwamnan wajen magance wasu daga cikin matsalolin da ke hana kasuwar gudanar da aiki cikin sauki.
|
1
|
<|title|>Majalisar Taraiya ta tabbatar da sabon shugaban NAHCON, Farfesa Saleh Usman
<|section|>news
A yau Alhamis ne Majalisar Taraiya ta tabbatar da nadin Farfesa Saleh Abdullahi Usman a matsayin shugaban Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON. Hakan ya zama cewa Farfesa Usman shi ne shugaban NAHCON na 6. Tabbatarwar ta zo ne bayan da kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar Dattawan ta tantance shi a ranar Talata. A wata sanarwa da Fatima Usara, kakakin NAHCON ta fitar a yau Alhamis, tabbatarwar ta nuna irin yarda da kwarewa Farfesa Usman Wajen aikin da aka bashi. Shi ma kuma ya nuna godiya ga majalisar tariya bisa wannan tabbatarwa inda ya nuna kwarin gwiwa yin aiki tuƙuru don tabbatar da yarda da aka yi da shi wajen yin aikin.
|
2
|
<|title|>Ƙarin farashin mai: Ba mu mu ka kar zomon ba — Gwamnatin Taraiya
<|section|>news
Gwamnatin Taraiya ta baiyana cewa ba ita ta kara farashin litar man fetur ba. A jiya Laraba ne kamfanin mai na ƙasa l, NNPCL ya sanar da ƙarin litar man fetur daga Naira 897 zuwa sama da Naira 1,000 a fadin ƙasar, lamarin da ya haifar da cece-kuce da kuma alla -wadai ga yan kasar. Sai dai kuma a hirar da ya yi da Daily Trust, Ministan Yaɗa Labarai da Tarbiyyar Al’umma, Mohammed Idris ya ce ba gwamnati ba ce ta kara farashin mai. A cewar Ministan, NNPCL ne ya kara farashin man duba da yanayin da ɓangaren mai ya samu kan sa a ƙasar. Mohammed ya kara da cewa ba gwamnati ba ce ta baiwa NNPCL umarnin ƙarin farashin man ba saboda “gwamnati ba ta da ikon kari ko ragin farashin mai bisa ga yarjejeniyar da ke kunshe a sabon kundin dokar mai,” Ya ce tun da aka cire tallafin mai a watan Mayun 2023, NNPCL ke cika gibin da ake samu don a saukaka farashin, “inda yanzu kuma NNPCL ya ce bashi da halin ci gaba da cike gibin.”
|
3
|
<|title|>NLC ta buƙaci a janye ƙarin farashin litar man fetur
<|section|>news
Shugaban Kungiyar Ƙwadago ta Ƙasa, Joe Ajaero ya yi kira ga gwamnatin taraiya da ta gaggauta janye ƙarin farashin litar man fetur da ta yi a jiya Laraba. A jiya ne dai kanfanin mai na kasa, NNPCL, ya sanar da karin farashin litar mai daga Naira 898 zuwa sama da Naira 1,000 a fadin ƙasar, lamarin da ya jefa yan kasar cikin damuwa. Sai dai kuma Daily Trust ta rawaito cewa Ajaero, a wata sanarwa da ya fitar a juya Laraba ya ce gwamnatin na ta kara farashin mai a duk wata yayin da ta gaza ƙaddamar da sabon mafi ƙarancin albashi. Hakazalika, a cewar sa, yanzu an bar kamfanonin mai masu zaman kansu su rika sayar da mai a farashin da su ka ga dama.
|
4
|
<|title|>Naira Miliyan 8.4 maniyyatan Kano za su fara ajiyewa domin aikin Hajjin baɗi — Danbappa
<|section|>news
Hukumar Jin Dadi da Walwalar Alhazai ta jihar Kano ta sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin wani ɓangare na kuɗin aikin Hajjin baɗi da kowanne maniyyaci zai ajiye. Shugaban hukumar, Alhaji Laminu Rabi’u Danbappa ne ya baiyana hakan yayin wat ganawa da jami’an aikin Hajji na kananan hukumomi a shelkwatar hukumar. A wata sanarwa da kakakin hukumar, Suleman Dederi ya fitar a jiya Litinin Kano, Danbappa ya ce Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON ce ta bada umarnin a sanar da Naira Miliyan 8.4 a matsayin kason farko na kuɗin aikin Hajjin 2025. Ya kuma hori maniyyatan da su tabbatar sun biya kudaden su a kan lokaci. Hakazalika Danbappa ya sanar da cewa NAHCON ta baiwa Kano kason kujerar alhazai 4,356, wanda a cewar sa, za a rarraba su a kananan hukumomi 44 na jihar. Ya kuma sanar da cewa jihar Kano ta fara shirye-shiryen aikin Hajjin na baɗi, inda ya yi fatan a yi shi cikin nasara.
|
5
|
<|title|>ABIN TAUSAYI: Kwastoma ta yanke jiki ta fadi bayan ta zubar da Naira miliyan 2.3 a wata kasuwa a Abuja
<|section|>news
Wata mata mai suna Rukayyat, ta yanke jiki ta fadi bayan da ta fuskanci cewa ta zubar da kuɗin ta naira miliyan 2.3 a kasuwar Abaji da ke Abuja. Matar, kamar yadda Daily Trust ta rawaito, ta fadi ne a ranar Juma’a da misalin ƙarfe 9:45 bayan da ta je kasuwar saro kayan abinci. Wani ganau, mai suna Yakubu Musa, wanda ya ce duk Juma’a matar na zuwa daga garin Auchi a jihar Edo, ya ce matar ta kira babu kudin nata ne bayan an kusan kammala auna mata hatsin da ta saya a buhuhuna. A cewar sa, ta na duba kudin ta ga babu sai ya yanke jiki ta fadi ta na ta rusa ihu, inda ta rika fadin cewa kuɗin na bashi ne ta ciyo don ta yi kasuwanci.
|
6
|
<|title|>Ƴan bindiga sun sace basarake a jihar Kebbi
<|section|>news
Ƴan bindiga sun kai wani hari a garin Kanya da ke ƙaramar hukumar Danko-Wassagu ta Jihar Kebbi a arewa maso yammacin Najeriya inda rahotanni suka bayyana cewa sun yi awon gaba da uban ƙasa na yankin da kuma aƙalla wasu mutane tara. BBC ta rawaito cewa ƴan bindigar sun kuma kashe mutum ɗaya da kuma raunata wasu mutane uku da yanzu haka ake kula da su a asibiti. Wannan lamari dai ya wakana ne a daren Asabar zuwa safiyar Lahadi da ta gabata, kamar yadda wani mazaunin yankin da ya buƙaci a sakaya sunansa ya bayyana, wa BBC. Ya ce : ”Da misalin ƙarfe ɗaya na daren Asabar ɓarayi suka shigo garin Kanya, inda suka kama mutane 10, ciki har da uban ƙasar Kanya, Alhaji isa ɗaya wanda aka kama tare da iyalensa. Sun tafi da mutum 10, sun kashe mutum ɗaya, sa’annan sun jikkata mutum biyu mace da namiji wanda yanzu haka suna kwance a asibiti.” Mutumin ya bayyana cewa mutanen yankin na zaune cikin halin fargaba da tashin hankali sakamakon jimamin da suke yi na wannan lamari da ya afku. Ya ƙara da cewa ya zuwa yanzu ba a samu yin magana da waɗanda suka sace mutanen ba, balle ma a fara tunanin yadda za a yi a dawo da su. Ya ce: ”Ba su tambayi komai ba sun dai shiga gidajen mutane suka tafi da waɗanda suka kama, kuma har yanzu ba a ji daga garesu ba.” Babban jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ƴansandan jihar Kebbi, ASP Nafi’u Abubakar ya tabbaar da faruwan lamarin inda ya ce a lokacin da rundunar ta sami labarin, jami’anta sun garzaya yankin amma ba su cimma ɓarayin ba. ”Ɓarayin sun ƙetaro ne daga jihar Zamfara, kuma mun sami rahoton cewa sun tafi da mutum tara bayan sun kashe mutum guda a lokacin harin.” In ji shi ASP Nafi’u Abubakar ya ƙara da cewa wannan harin dai ya zo ne a lokacin da aka kwashe tsawon watanni ba a sami aukuwar irin haka ba a yankin amma a halin yanzu rundunar ta baza jami’anta a sassa daban-daban na yankin domin tabbatar da zaman lafiya. Jihar Kebbi dai na cikin jihohin arewacin Najeriya da suka daɗe suna fama da matsalar rashin tsaro inda ƴan bindiga ke kai hare-hare akai-akai su kuma sace mutane domin karɓar kudin fansa, amma a baya baya nan hukumomin tsaro sun yi iƙirarin cewa lamarin ya ɗan yi sauƙi sakamakon tsauraran matakai da suka ce suna ɗauka kan ƴan bindigar da suka addabi yankin.
|
7
|
<|title|>Tinubu ya jajanta wa wadanda haɗarin jirgin ruwa ya shafa a Niger
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sakon ta’aziyya zuwa ga gwamnati da al’ummar jihar Niger bisa hatsarin jirgin ruwa da ya faru a ranar Talata a karamar hukumar Mokwa dake jihar. Jirgin ruwan wanda rahotanni suka bayyana cewa yana dauke da mutane 300 yawancin su mata da kananan yara yayi hatsari a kogin Gbajibo. Yayin da aka ceto mutane 150, an kuma samu gawar mutane 25. A sanarwar da mai bai wa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya jajantawa iyalan wadanda lamarin ya shafa inda yayi addu’ar Allah ya jikansu. Shugaban kasar ya kuma bada umarni ga hukumar kula da hanyoyin ruwa ta NIWA da ta binciki musabbabin samun yawaitar hatsarin jirgin ruwa a jihar Niger da ma kasa baki daya. “Shugaban kasa Tinubu ya godewa ma’aikatan bada agajin gaggawa wadanda suka taimaka wajen gano ragowar mutanen”, inji sanarwar.
|
8
|
<|title|>Ƴan Nijeriya ba za su iya jure mulkin APC sama da 2027 ba — Kwankwaso
<|section|>news
Shugaban jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso ya nuna kwarin gwiwa cewa ƴan Nijeriya za su canja yanayin mulkin kama-karya da APC ke yi a 2027. Kwankwaso ya fadi hakan ne a yayin da ya ke karɓar mabiya jam’iyyar APC 977 na Ƙaramar Hukumar Dala da su ka bar jam’iyyar zuwa NNPP a Kano a yau Alhamis a gidan sa da ke Miller Road. A cewar Kwankwaso, gwamnatin APC ta gaza gurin cika alkawuran da ta daukar wa ƴan Nijeriya, inda ya yi kira ga ƴan ƙasa da su yi ƙoƙari su canja gwamnatin a 2017. “Talauci, yunwa, rashin tsaro da rashin aikin yi sai ƙaruwa su ke. Magidanta ba sa samu su ciyar da iyalan su. “Wannan lokaci ne da ƴan Arewa da ma Nijeriya baki daya za su tashi tsaye su kawo canji da kan su. “Su na ganin ba za a iya canja su ba saboda su na da tsaro da hukumar zabe, to idan guguwar canjin ta bisa su da kan su za su yi gudun famfalaƙi,” in ji Kwankwaso
|
9
|
<|title|>Ƴansanda sun kama wasu bisa zargin yunƙurin kai hari a bikin ranar ƴanci a Abuja
<|section|>news
Jami’an rundunar ƴansandan birnin tarayya Abuja sun kama wasu mutane 4 da ake zargi da shirya kai hari hukumomin gwamnati da rukunin gidaje a ranar bikin ‘yanci. A cikin wata sanarwa da rundunar ta fitar a ranar Alhamis, mai magana da yawun rundunar, Josephine Adeh ta bayyana sunayen waɗanda ake zargin da suka haɗa da Yau Sani wanda aka fi sani da Baba (tsohon wanda kotu ta taba samu da laifi) da Nuhu wanda aka fi sani da Giwa da Kabiru Mohammed da Yusuf Hassan. Adeh ta ce waɗanda ake zargin sun kuma amsa laifin yin garkuwa da mutane da dama a birnin tarayya Abuja da Kaduna da Niger tare da kashe mutane 7. Ta ce, “Sashin yaki da garkuwa da mutane na rundunar ‘yan sandan Abuja, a ranar 1 ga watan Oktoba, bisa rahotan sirri da ya samu ya bibiya tare da kama kasugurman masu satar mutane wadanda suka addabi birnin tarayya Abuja”. ” Wadanda ake zargin sun amsa laifin yin garkuwa da mutane tare da kisan mutane 7 a Abuja da kewayenta. Adeh ta ce bayan kama mutanen, sun jagoranci ‘yansanda zuwa dajin da soke boye makamansu. Ta kara da cewa an kwato bindigogi kirar AK-47 guda 4 da Alburusai 175.
|
10
|
<|title|>Dalilin da ya sa aka kori Seaman Abbas daga aiki — Rundunar Soji
<|section|>news
Rundunar tsaro ta kasa a Najeriya, ta yi ƙarin bayani game da dalilan sallamar sojan ruwan nan Seaman Abbas Haruna daga aiki. A wajen wani taron manema labarai da ta kira a Abuja, hedikwatar tsaron ta ce an sallami Seaman Abbas daga aiki ne bayan wata kotun soji ta same shi da wasu laifuka uku da ake zarginsa da aikatawa. Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, Birgediya Janar Tukur Gusau, ya shaida wa BBC cewa, Seaman Abbas, ya yi wasu abubuwa na rashin ɗa’a. Abubuwan sun hada da kin bin umarnin kwamandan bataliya da kuma yin surutu a lokacin da kwamandan ke jawabi ga sojoji. A cewar Gusau, da kwamandan ya umarci Abbas ya kai kansa wani ɗaki da ake tsare mutane idan sun yi laifi sakamakon kaifin da ya yi, to sai yaƙi zuwa. “Daga nan ne sai kwamandan ya ce tun da yaƙi zuwa to a karɓe bindigar dake hannunsa, to maimakon ya miƙa bindigar sai ya fara harbe-harbe har sai da fitar da harsashi 16, to Allah ya kiyayye bai harbi kowa ba”. Tukur Gusau, ya ce a ɓangaren aikin soja ba a wasa da batun bindiga ko harsashi, domin harsashi ɗaya idan soja ya fitar sai an bibiya an ga me yasa ka fitar da shi. Jami’in hulda da jama’a na rundunar tsaron ta Najeriya, ya ce, “Bisa ga wannan aka tuhumeshi inda aka tura shi kotun soja kuma koda aka kai shi ya amsa laifinsa, a kan haka ne kotu ta tuhumeshi da aikata laifuka uku”. Ya ce a watan Fabrairun 2023, kotun ta kore shi daga aiki.
|
11
|
<|title|>Hisbah ta kama katan 18 na barasa a wani kanti a Kano
<|section|>news
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ce ta kama katan 18 na barasa a wani shago dake titin Sultan Road a yankin Nasarawa GRA. Mukaddashin shugaban hukumar, Malam Mujahid Aminudeen ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya aikowa DAILY NIGERIAN HAUSA a yau Laraba. Ya kara da cewa hukumar ta kai samame wasu gidaje da ake zargin ana ta’ammali da miyagun kwayoyi inda aka samu kayan maye tare da kama maza 9 da mata 3. “Cikin taimakon Allah, Operation ‘Ba Barasa’ sun tafi Operation kuma Allah ya basu nasara, wanda suka yi kokari suka samo wadannan gidaje da muke kuka da su a can bayan rukunin gidajen Kwnakwasiyya. Wanda gida ne zaka gani an mayar da shi Logging, ga mata ga maza, ana ta masha’a . Alhamdulillah, sun samo mata wajen guda tara maza guda 3”, inji Malam Mujahid. Mukaddashin shugaban hukumar, ya ce kofarsu a bude take ga mutanen wajen su zo su sanar dasu duk inda suke zargin ana aikata ba daidai ba domin daukar mataki. Sannan ya godewa al’umma bisa hadin kan da suke basu wajen kawar da ayyukan alfasha a jihar ta Kano.
|
12
|
<|title|>Daily Trust ta bada haƙuri kan labarin yarjejeniyar SAMOA
<|section|>news
Jaridar Daily Trust ta bayar da haƙuri kan labarin da ta yi na yarjejeniyar Samoa, wanda ya tayar da ƙura. BBC ta rawaito cewa a wata sanarwa da ta fitar, mai taken, Yarjejeniyar Samoa: Muna bayar da haƙuri, ta ce, “A jaridarmu ta 4 ga Yulin 2024, babban labarinmu mai taken, “LGBT: Najeriya ta shiga yarjejeniyar biliyan $150 da Samoa”, labarin ya tayar da ƙura a faɗin ƙasar. Wannan ya sa gwamnatin tarayya ta shigar da ƙara a gaban hukumar sauraron ƙararrakin da suke da alaƙa da jaridu wato National Media Complaints Commission (NMCC), wanda aka fi sani da Ombudsman.” Sanarwar ta ƙara da cewa “bayan sauraron kowane ɓangare, NMCC ta gano cewa akwai kura-kurai a labarin, sannan an kauce daga wasu ƙa’idojin aikin jarida waɗanda ya kamata kowace jarida ta kiyaye. Mun amince da wannan matsaya ta NMCC. Muna ba gwamnatin tarayya haƙuri, sannan muna ba masu karanta jaridunmu da dukkan sauran mutane haƙuri bisa kuskuren da muka yi.” Dangane kuma da hanyoyin da jaridar ke bi wajen tantance labaranta, jaridar ta ce “hanyoyin da muke bi wajen tantance labari suna da inganci, kuma sun taimaka mana wajen gudanar da ayyukanmu na sama da shekara 25. Amma duk da haka, bayan wannan kuskuren, mun sake dubawa tare da inganta su. “A matsayinmu na gidan jarida, burinmu shi ne samar da labarai masu inganci da samar da haɗin kan ƙasa da tsaronta da kuma tabbatar da cigabanta. Muna yin hakan ne ta hanyar fitar da labarai da za su taimaka wa mutane wajen fahimtar duniya da kuma bayar da damar tafka muhawara da kuma bin diddigin harkokin shugabanci. Daga ƙarshe jaridar ta sanar da cewa ba ta yi labarin ba da nufin nuna hamayya ga wata gwamnati “ba ma goyon baya, ko kuma adawa da kowace gwamnati ko jam’iyya, ko ɗaiɗaikun mutum. Burinmu shi ne samar da gaskiya domin ilimantar da mutane.Amma kamar sauran jaridu, dole wasu lokutan za mu iya yin kuskure,” kamar yadda Daily Trust ta ƙara haske.
|
13
|
<|title|>Budaddiyar Wasika Ga Gwamnatin Najeriya ‘An Bar Jaki Ana Dukan Taiki Akan Lafiya’
<|section|>news
Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu. Cikin girmamawa gareku shuwagabanni da Jami’o’in lafiyar na kasa ta Najeriya baki daya. Na ɗauki alkalami na ne domin nayi kira gareku akan wani ganganci da kantafi da rayukan al’umma da naga hukumar haraji ta Najeriya tayi a wani asibiti mai zaman kansa a birnin kano wato Best Choice specialist Hospital dake unguwar Gadon Kaya kan randabawud din Tal’udu. Wasu daga cikin marasa lafiya da wasu iyaye sun kawo wa jaridar Alfijir labarai korafi akan yadda jami’an hukumar tattara harajin suka zo tare da jam’i an tsaro da bindigogi suna musu barazana akan sai dole sun tashi sun fita daga cikin asibitin bayan bala’in da suke ciki na rashin lafiya, ga kuma sun yi yawo wurare da dama a garin Kano sun rasa inda za a iya samun gadon kwanciya musamman a bangaren larurar da ta shafi yara da jarirai sai nan ɗin! Babban abin takaici ma shine wasu daga cikin likitoci da ke Kano da ma wasu jahohin sun tsunduma yajin aiki akan hakkokinsu, maimakon wannan hukuma tayi aiki da hankali wajen taimakawa al’umma domin jin kansu, a a sai kokari take wajen kara nakasa rayuwar wadannan marasa lafiyar dake asibitin, ko kuma ma hallaka su! Matsalar haraji dake tsakaninku da asibiti matsala ce da ta shafe ku, ba abinda ya shafi wadanda suka zo neman lafiya asibitin bane! Don haka muke kira ga shuwagabanni na wannan kasa ta mu mai albarka, da hukumar kare hakkin bil’adama kan wannan cin zarafin da aka yiwa Al’umma da akawo musu ɗauki cikin gaggawa. Ku kuma hukumar tattara haraji Ku dubi Allah ku canja hanyar da zaku bi wajen neman hakkinku! Domin inda hakkin ku ya kare nan fa na wasu ya fara. Idan da ya’yanku ne ke zuwa asibitin ba na talakawa ba da ai ba zaku yi hakan ba! Kukan Kurciya Jawabi Ne. Sakon Editan Jajidar Alfijir labarai Mai Biyayya A Gareku
|
14
|
<|title|>Gwamna Abba ya ɗauki nauyin rayuwar marayu 95 a Kano
<|section|>news
A wani ɓangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai, gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sanar da daukar nauyin rayuwar marayu 95 a Kano. Gwamnan ya sanar da wannan abun alheri ne a lokacin liyafar cin abinci ta musamman tare da marayun 95 a gidan marayu na jihar tun bayan da iyayensu su ka rasu. Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Dawakintofa, ya fitar, ta ce Yusuf ya ayyana cikakken ɗaukar nauyin rayuwar marayu 95 daga yanzu. “Ina so in sanar da cewa mun dauki nauyin dukkan marayu 95 da ke zaune a wannan gida, za mu dauki nauyin karatunsu tun daga firamare har zuwa manyan makarantu, lafiyar su, cin su da shan su da sauran bukatu na yau da kullum har tsawon mulkina”. “Yanzu ku ‘ya’yana ne, zan kula da ku a matsayin nawa, za ku fara jin dadin rayuwa in sha Allahu” gwamnan ya tabbatar. Gwamnan ya bada tabbacin cewa har zuwa karshen wa’adin mulkin sa, za a dauki marayun a matsayin mutane masu matukar muhimmanci tare da cikakken amfani, kulawa da gata. Ya kara da cewa gwamnatin jihar za ta bai wa yaran damar kaiwa ga gaci a rayuwarsu.
|
15
|
<|title|>Zan iya rantsuwa da Al-ƙur’ani ban yi sata ba a lokacin da na ke Gwamna — El-Rufai
<|section|>news
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru El-Rufai ya ce a shirye ya ke da ya rantse da Al-ƙur’ani kan cewa bai yi sata ba a lokacin da ya ke mulkin jihar. Daily Trust ta rawaito cewa El-Rufai ya ce ya shiga siyasa ne don ya hidimtawa al’umma ba wai don neman kudi ko satar dukiyar jama’a ba. Trust ta ce ya yi bayanin hakan ne a yayin wani shirin Hausa na Gidan Rediyon Freedom a jihar Kaduna a yau Talata. El-Rufai ya yi bayanin cewa ya wadatu da abinda ya ke da shi tun kafin ya zama Gwamna. A tuna cewa majalisar dokokin jihar Kaduna dai ta yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta karkatar da Naira Biliyan 423 a lokacin mulkinsa na shekaru 8. Tsohon Gwamnan da hadiman sa sun musanta zargin na majalisar. Ya ce, “Na yi shiru ne kawai don ganin yadda abubuwa za su kasance, amma ni a ko da yaushe ina rokon Allah ya taimake ni a duk abinda nake a rayuwata, a matsayina na dan Adam, a koyaushe ina kokarin kaucewa yin ba daidai ba ko cin amanar al’umma.” Sannan tsohon Gwamnan ya ce ana gayyatar mutanen sa zuwa ICPC da EFCC don kawai a bata musu suna, a don haka ya bar lamarin ga Ubangiji.
|
16
|
<|title|>Matsin rayuwa: Aiki na ke tuƙuru dan samarwa ƴan Nijeriya mafita mai ɗorewa — Tinubu
<|section|>news
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar wa ‘yan Najeriya kudirin gwamnatinsa na samar da mafita mai dorewa domin rage musu radadin matsin rayuwa da suke ciki. Ya bayar da wannan tabbacin ne a jawabinsa da ya yi wa ƴan kasa kan bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ƴancin kai. “Ina sane da halin kunci da da yawa daga cikin ku ke fuskanta a cikin waɗannan lokuta masu ƙalubale. “Gwamnatinmu ta san cewa yawancinku suna fama da tsadar rayuwa da neman aiki mai tsoka. Ina so in tabbatar muku cewa ina jin koken ku,” inji shi. Tinubu ya roki ‘yan Najeriya da su yi hakuri “yayin da gyare-gyaren da muke aiwatarwa ke nuna alamun nasara, kuma mun fara ganin haske a gaba.”
|
17
|
<|title|>Dakarun mu sun kashe kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji 300 – Tinubu
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Tinubu ya ce gwamnatin sa na samun nasara a yakin da take da ‘yan ta’addan Boko Haram dake addabar Arewa maso gabas da ‘yan fashin daji dake Arewa maso yamma. A jawabin da yayiwa ‘yan Nijeriya a bikin ranar ‘yancin, shugaban kasar ya ce kafin ya hau karagar mulki watanni 16 da suka gabata, kasar nan na fama da matsin tattalin arziki da rashin tsaro. Shugaban kasar wanda ya ce, garambawul din da ake yi ya zama dole don sai ta kasar, yayi nuni da cewa “Mun yanke shawarar yin garambawul ga tsarin tattalin arzikin mu da tasawirar tsaro”. Shugaban kasar ya tabbatar da cewa gwamnatin sa ta kashe manyan kwamandojin Boko Haram da na ‘yan fashin daji inda ya kara da cewa sojoji sun kashe sama da kwamandojin Boko Haram da ‘yan fashin daji 300 a Arewa Maso Gabas da Arewa maso yamma.
|
18
|
<|title|>Tinubu ya rantsar da Kekere-Ekun a matsayin babbar Joji ta ƙasa
<|section|>news
Shugaban ƙasa, Bola Tinubu ya rantsar da Kudirat Kekere-Ekun a matsayin babbar mai shari’a ta ƙasa. Bikin rantsarwar ya gudana ne a babban ɗakin taro na fadar shugaban ƙasa dake birnin tarayya, Abuja a yau Litinin. Rantsar da Kekere-Ekun a matsayin cikakkiyar alkalin alkalan Nijeriya ya biyo bayan tabbatar da ita da majalisar dattawa tayi a makon da ya gabata. A watan Agustan da ya gabata, Majalisar Harkokin Shari’a ta kasa (NJC) ta baiwa Shugaba ƙasa Tinubu shawarar naɗa mai Shari’a Kekere-Ekun a matsayin wacce zata gaji tsohon babban jojin Najeriya, Mai Shari’a Olukayode Ariwoola. Kekere-Ekun ce babbar jojin Najeriya ta 23 kuma mace ta 2 da ta taɓa riƙe wannan mukami. Maryan Aloma Mukhtar ce mace ta farko wacce ta rike mukamain babbar mai shari’a ta Najeriya tsakanin watan Yulin 2012 da Nuwambar 2014.
|
19
|
<|title|>Rundunar yansandan jihar Kano ta kama mutane 89 da ake zargi da aikata laifuka
<|section|>news
A kokarin ta na magance ayyukan bata gari a jihar Kano, rundunar ‘yansandan jihar ta kama mutane 89 bisa zargin aikata laifuka daban-daban. Kwamishinan ‘yansandan jihar, Salman Dogo ne ya bayyana hakan yayin da yake yiwa manema labarai jawabi a shelkwatar rundunar dake Bompai, Kano a ranar Litinin. Dogo ya ce laifukan da mutanen suka aikata sun hada da garkuwa da mutane don neman kudin fansa da fashi da makami da ta’ammali da miyagun kwayoyi. Ya ce, an yi kamen ne a wurare daban daban na jihar, daga ranar 12 ga watan Satumba zuwa yau inda ya kara da cewa an mika mutane 53 da ake zargi gaban kotu a yayin da 36 ake kan bincike a kansu. Kwamishinan wanda ya samu wakilcin SP, Abdullahi Haruna Kiyawa, mai magana da yawun rundunar, ya ce an kwato makamai masu hatsari daga wajen wadanda ake zargin da suka hada da bindiga da adda da wukake. Sannan ya ce rundunar za ta ci gaba da aiwatar da aikin ta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada. “A don haka, rundunar ‘yansanda zata ci gaba da sauke nauyin dake kanta kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanada”, inji Kwamishinan.
|
20
|
<|title|>Gwamnatin Taraiya ta baiwa ƙungiyoyin kwadago motoci masu amfani da gas guda 64
<|section|>news
Gwamnatin tarayya ta mika motocin bas guda 64 masu amfani da gas (CNG) ga wakilan kungiyoyin kwadago da suka hada da TUC, NLC, da kungiyar dalibai ta kasa NANS. An gudanar da mika motocin bas din ne a jiya Lahadi a babban dakin taro na fadar gwamnati da ke Abuja, a wani bangare na bikin cikar Najeriya shekaru 64 da samun ‘yancin kai. Wale Edun, Ƙaramin Ministan Tattalin Arziki na Kasa kuma Ministan Kudi ne ya jagoranci tawagar gwamnati wajen bikin mika motocin. Edun ya ce idan aka fara amfani da motocin bas din za su rage tsadar zirga-zirgar ababen hawa a kasar, wanda hakan zai sa a samu ingantaccen tsarin motocin haya da araha. Comrade Nuhu Toro, Babban Sakatare kuma Shugaban Hukumar TUC; Comrade Lucky Emonefe, shugaban NANS, da Comrade Uche Ekwe, shugaban sashin kula da harkokin kasa da kasa, NLC, sun yabawa Tinubu kan wannan karimcin. Sun yi kira da a samar da karin motocin bas din masu amfani da CNG ga jama’a. Mista Toro ya godewa shugaban kasa kan aiwatar da sabon mafi karancin albashi na N70,000 na kasa.
|
21
|
<|title|>Ibtila’in da ke faruwa a Nijeriya na neman fin karfin mu — Red Cross
<|section|>news
Kungiyar agaji ta Red Cross ta Najeriya ta ce duk da cewa tana da masu aikin sa kai sama da dubu 800 a duk fadin kasar, ibtila’i da bala’o’i da ke faruwa a kasar na neman fin karfin ta. Shugaban Red Cross ma kasa, Prince Oluyemisi Adeaga ne ya bayyana haka a Legas yayin taron tara gudunmawa na 2024 da aka gudanar a Legas a ranar Asabar. Saboda haka Adeaga yayi kira ga masu hannu da shuni da su kara dagewa da bada tallafi wajen ayyukan Red Cross don taimakawa ƴan Najeriya da suka rasa matsugunansu. Adeaga ya bayyana cewa har yanzu Najeriya ba ta farfado daga bala’in ambaliyar ruwa na 2022 ba sai ga lamarin ya sake afkuwa a 2024, inda ya kara da cewa matsalar jin kai a Maiduguri kadai bayan ambaliyar ruwan da aka yi a baya-bayan nan ta wuce tunani.
|
22
|
<|title|>NYSC: Gwamnatin tarayya ta kara alawus din masu yi wa kasa hidima
<|section|>news
Gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus na wata-wata na masu yinwa ƙasa hidima daga Naira dubu 33 zuwa Naira dubu 77. An sanar da karin alawus din ne a wata sanarwa da shafin kula da shirin na masu yiwa kasa hidima ya wallafa a Facebook. Sanarwar ta ce, “Gwamnatin tarayya ta amince da karin alawus ga masu yiwa kasa hidima zuwa Naira dubu 77 farawa dafa watan Yuli na 2024. “An dau matakin ne bisa amincewa da dokar mafi karancin albashi ta 2024. Hakan na dauke ne cikin wata wasika daga hukumar kula da albashi ta kasa mai dauke da kwanan watan 25 ga watan Satumba 2024 wacce Mista Ekpo Nta ya sanyawa hannu. ” Kafin hakan, darakta janar na shirin NYSC, Janar YD Ahmed, ya kai ziyara ga shugaban hukumar kula da albashin inda ya nemi a kara lura da walwalar masu yiwa kasa hidima.”
|
23
|
<|title|>DA ƊUMI-ƊUMI: Ba makawa Tinubu zai yi canje-canje a majalisar ministoci — Fadar shugaban ƙasa
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana aniyar sa ta yin garambawul a majalisar ministocinsa. Shugaban ya kuma kalubalanci Ministocin da kada su kasance masu jin kunya a kafafen yada labarai, sai dai ma su fito su nuna ayyukan ma’aikatun su. Daily Trust ta rawaito cewa da ya ke jawabi ga manema labarai a fadar shugaban kasa da ke Abuja a yau Laraba, Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin yada labarai da dabaru ya koka da cewa gwamnatin Tinubu na yin abubuwa da dama, amma ‘yan Najeriya ba su sani ba. Ya ce, “Shugaban kasa ya bayyana aniyar sa na yin garambawul a majalisar ministocinsa kuma zai yi. Ban sani ba ko yana so ya yi kafin Oktoba, amma tabbas zai yi. Abin da zan ce ke nan, amma bai fada mana wane lokaci ne ba.”
|
24
|
<|title|>UNGA 79: Tinubu ya yi kira ga kasashen duniya su yafe wa Nijeriya bashin da ake bin ta
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Tinubu yayi kira da shugabannin kasashen duniya da su bada muhimmanci wajen yafewa Nijeriya bashin da ake bin ta. Shugaban kasar ya kuma bukaci majaisar dinkin duniya da ta bada muhimmanci ga alakar kasuwanci tsakanin kasashe ba tare da nuna bangaranci ba kamar yadda yake a tsarin shiga a dama da kowa da daidaito gami da hadin kai. Tinubu wanda shi ne shugaban kungiyar ECOWAS ya yi kiran ne a jawabin da ya gabatar a zauren majalisar dinkin duniya a taron ta karo na 79 a birnin New York. Shugaban kasar, wanda ya samu wakilcin mataimakin sa, Kashim Shettima, ya ce kasashen na kudancin duniya baza su samu ci gaban tattalin arziki ba idan ba a rage musu bashin da ake bin su ba. A wata sanarwa da mai taimakawa shugaban kasa kan fannin kafafen yada labarai a ofishin mataimakin shugaban kasa, Stanley Nkwocha, ya ce shugaban Nijeriyar ya jawo hankalin shugabannin duniya kan yadda bashin da ake kasashe ke hana su biyan bukatun yan kasashen su. A rahotan ofishin kula da basussuka na kasa, bashin da ake bin Nijeriya na cikin gida da na waje ta kai Naira Tiriliya 121.67. Da yake jawabi kan kalubalen bashin, Tinubu ya ce, “Haka abin yake, dole ne mu tabbata duk wani garambuwl ga tsarin hada hadar kudade ya hada da rage matakan bashin da ake bi don bada dama wajen ayyukan ci gaba. ” Kasashen kudancin duniya baza su iya samun ci gaban tattalin arziki ba ba tare da an rage musu bashin da ake bin su ba”, inji shi.
|
25
|
<|title|>BUA ya bada tallafin Naira Biliyan 2 ga wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri
<|section|>news
Error fetching article: Message: Stacktrace: #0 0x59cba9f48cea #1 0x59cba99f95f0 #2 0x59cba9a4aa33 #3 0x59cba9a4ac21 #4 0x59cba9a99274 #5 0x59cba9a7068d #6 0x59cba9a96660 #7 0x59cba9a70433 #8 0x59cba9a3cea3 #9 0x59cba9a3db01 #10 0x59cba9f0db3b #11 0x59cba9f11a21 #12 0x59cba9ef4c32 #13 0x59cba9f12594 #14 0x59cba9ed8eef #15 0x59cba9f36d98 #16 0x59cba9f36f76 #17 0x59cba9f47b36 #18 0x7e08c5cb4ac3
|
26
|
<|title|>Labarin Samoa: Kun tafka kuskure — Kwamitin sa ido kan aikin jarida ya tabbatarwa Daily Trust
<|section|>news
Kwamitin karɓar Ƙorafe-ƙorafe kan Kafafafen Yaɗa Labarai na Kasa (NMCC), ya fitar da rahotonsa kan taƙaddamar zargin goyon bayan auren jinsi Yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta sanyawa hannu ta Samoa. Kwamitin wanda gogaggun yan jarida da lauyoyi ke yiwa shugabanci ya ce kamfanin Daily Trust ya tafka kuskure a wancan labarin akan Yarjejeniyar ta Samoa. Binciken ya biyo bayan korafin da Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a ta Tarayya ta yi a kan jaridar Daily Trust. Hukumar, a cikin rahotonta mai shafuka 19, ta ce bayan ta binciki korafin gwamnati, da kuma martanin da jaridar tayi, ta gano labarin da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yarjejeniyar SAMOA a matsayin kuskure, tare da umartar Jaridar ta nemi afuwar Gwamnatin Tarayya bisa abin da rahoton na su ya jawo mata.
|
27
|
<|title|>Gwamnatin tarayya za ta gina tituna 14 a inda ambaliyar ruwa ta yi barna
<|section|>news
Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da aikin gina tituna 14 da gadoji wanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar Ekiti da Adamawa da Kebbi da jihar Enugu. Ministan ayyukan, David Umahi ne ya bayyana hakan yayin yiwa manema labarai na fadar shugaban kasa bayani bayan zaman majalisar zartarwar. Ya ce sauran jihohin sun hada sa Cross River da Ondo da jihar Osun da Ebonyi da Abia da jihar Imo. Ya ce, an bada aikin kwangilar gina hanyoyin ne kari kan kwangilar gyara gadar Gamboru dake Gamboru-Ngala da Kala-Balge a jihar Borno. Minsitan ya ce majalisar ta kuma amince da sabuwar kwangilar gina hanyar Maraban-Kankara da Funtua a jihar Katsina. Haka kuma, majalisar ministocin karkashin jagorancin shugaba Tinubu ta amince da gina hanyar Afikpo zuwa Uturu-Okigwe a jihar Ebonyi da Abia da jihar Imo. “Majalisar zartarwa ta kasa ta amince da fitar da Naira Biliyan 80 don kammala wannan aikin, wanda jimilla ya kama biliyan 280.” Daily Nigerian
|
28
|
<|title|>Lokaci ya yi da gwamnati za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur — Dangote
<|section|>news
Mamallakin matatar mai ta Dangote, Aliko Dangote, ya ce lokaci ya yi da gwamnatin tarayya za ta kawo karshen biyan tallafin man fetur. A yayin tattaunawa da jaridar Bloomberg a ranar Litinin, Dangote ya ce tallafin mai zai kai gwamnati ga “Biyan abinda bai kamata ta rika biya ba” don haka akwai bukatar kawo karshen sa. Daily Nigerian ta rawaito cewa dan kasuwar ya jadadda cewa gwamnatin Tinubu baza ta iya jure biyan tallafin man ba. Dangote ya ce: “Ina tunanin yanzu ne lokacin janye tallafin mai sabora duk kasashe sun dena biyan tallafin. ” Gwamnati baza ta iya biyan tallafin mai ba,” in ji shi.
|
29
|
<|title|>YANZU-YANZU: Alkaliya ta janye daga zaman sauraron ƙarar Nnamadi Kanu
<|section|>news
Binta Nyako, Alkaliyar babbar kotun tarayya ta janye daga zaman sauraron karar da ake tuhumar jagoran haramtacciyar kungiyar IPOB, Nnamadi Kanu. Alkalai dai sun saba janye wa daga sauraron shari’a saboda zargin son rai ko nuna bangaranci. A yayin zaman kotun a yau Talata, Nnamadi Kanu ya shaidawa Alkaliyar cewa bashi da kwarin gwiwa kan ta game da shari’ar, mai yiwuwa shi ne dalilin da ya sa ta janye.
|
30
|
<|title|>Hanya ɗaya tak da za a inganta rayuwar yaran da ke barace-barace a Kano da Arewa — Daga Mustapha Hodi Adamu
<|section|>news
Ni Ko ina ganin da gwamnatin Kano za ta haɗa kai da Alhaji Aliko Dangote, Alhaji Aminu Dantata da Alhaji Abdussamad Isyaku Rabi’u, a gina katafarun makarantun kwana na firamare da sakandire don yaran nan maza da mata da ke barace-barace a kwararo-kwararo a cikin birnin Kano, da an samu ci gaba wajen ilimi da zaman lafiya a jihar. In har Dangote da Dantata za su iya bada gudummawar Naira biliyan 1.5 kowannen su a wata jiha da ba tasu ba, to kuwa idan aka tuntube su akan wannan gagarumin aiki, tabbas ina da yaƙinin za su bada gudunmawa mai gwaɓi. Yawaitar ƙananan yara da ke barace-barace a unguwanni da tituna a jihar Kano ya damu kowa kuma ya sanya fargabar illar hakan a nan gaba. Waɗannan yaran barazana ne ga jihar Kano da ma Arewa baki daya. Amma idan aka kwashe su, aka kai su makarantun, aka rika koya musu karatu da sana’o’i a lokacin da su ke karatun to za a taimaka wa rayuwar su kuma su ma za su taimakawa al’umma. In ba haka ba, da wasa da wasa za su zamo wa jihar gagarumar matsala (Allah Ya kiyaye). Idan gwamnati ta tuntubi waɗannan attajirai da na lissafo a sama, ta kuma haɗa da ƴan siyasar mu da su ka shahara a fannin mulki kamar irin su tsofaffin gwamnonin Kano – Mal. Ibrahim Shekarau, Dr Rabi’u Musa Kwankwaso da Dr Abdullahi Umar Ganduje. Sai kuma masu ci a yanzu irin su Sanata Barau Jibrin, Sanata Kawu Sumaila, Sanata Rufai Sani Hanga da sauran ƴan siyasa da masu hannu da shuni, akan su bada gudunmawa wajen gina waɗannan makarantu, in sha Allahu za su taimaka. Haka zalika idan an tashi gina makarantun, sai a gina su a shiyyoyi uku na Kano – Kano ta Tsakiya, Kano ta Arewa da Kano ta Kudu, sannan a fitar da tsari mai kyau da zai ɗorar da zaman waɗannan makarantu har illa ma sha Allah. Khalifa Dankadai kadai idan aka bashi project din nan zai yi delivering sosai domin ya san kan harkar empowering almajirai. Allah Ya sa gwamnati ta ji ta kuma dauki wannan shawara ta wa. Mustapha Hodi Adamu ya rubuta wannan rubutu da ga jihar Kano kuma za a iya samun sa a kan – [email protected]
|
31
|
<|title|>Tallafin ambaliya: Naira biliyan 4 ne su ka shigo asusun mu a halin yanzu — Zulum
<|section|>news
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya ce kawo ya zu, kuɗin da su ka shiga asusun jihar na tallafawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a jihar bai wuce Naira biliyan N4.4 ba. Daily Trust ta rawaito cewa gwamnatin jihar dai ta bude asusun domin tallafa wa wadanda ambaliyar ruwan ta shafa. Rahotanni sun nuna cewa kuɗin da aka tara na gudummawa ya kai Naira biliyan 13. Sai dai kuma Zulum ya baiyana cewa Naira biliyan 4.4 kawai su ka shigo asusun. “Mun samu alkawari na Naira Biliyan 13, 500, 000; kodayake daga jiya Lahadi, mun karbi jimillar kudi Naira Biliyan 4, 4441, 494, 902.81. Duk abinda aka tura wannan asusun za mu sanar da al’umma,x in ji Zulum. Gwamnan, wanda ya bayyana hakan yayin da yake kaddamar da kwamitin mutane 35 na rabba tallafin rage radadin a birnin Maiduguri a ranar Litinin, ya bukaci mambobin kwamitin su yi aikin da gaskiya. ” Dole ne mu yi taka-tsantsan da dukkan abinda aka bamu”, inji shi. Gwamna Zulum ya kara da cewa, “Dole ne mu tabbatar da an yi amfani da duk Naira daya da aka bayar don rage radadi ta isa ga wadanda abin ya shafa” Gwamnan ya kuma umarci a biya kudin alawus na mambobin daga asusun gwamnatin Borno ba asusun tallafin ba. Gwamnan ya umarci a bada tallafin dukkan sa ga wadanda ambaliyar ta shafa. Daidaiku da kungiyoyi ne dai suka bada gudunmawa ga wadanda iftila’in na Maiduguri ya shafa.
|
32
|
<|title|>Zaben Edo: Nasarar APC ta nuna cewa ƴan Nijeriya sun gamsu da salon mulkin mu — Tinubu
<|section|>news
Shugaban kasa Tinubu ya taya murna ga dan takarar jam’iyyar APC, a zaben Gwamnan jihar Edo, Sanata Monday Okpebholo bisa nasarar lashe zaben da ya yi. A juya Lahadi ne hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa, INEC, ta sanar da Sanata Okpebholo a matsayin wanda ya lashe zaɓen. A sanarwar da mai baiwa shugaban kasa shawara kan fannin yada labarai da dabarun mulki , Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yabawa shugabannin APC na kasa da na jihar Edo da Gwamnonin jam’iyyar bisa aiki tukuru wajen nasarar ta a zaɓen. Shugaban ya ce, nasarar ta nuna goyan bayan da al’umma ke bai wa manufofin gyaran tattalin arziki, da ma salon mulkin da APC. Shugaban ya kuma yi kira ga wadanda su ka samu rashin nasara da su yi amfani da hanyoyin shari’a wajen mika kokensu. Shugaban ya kuma godewa INEC da jami’an tsaro bisa tabbatar da an yi zaben cikin nasara. “Ina yabawa hukumar zabe ta INEC da hukumomin tsaro bisa aiki ba dare ba rana wajen gudanar da zaben cikin lumana”
|
33
|
<|title|>Kwalara ta hallaka mutane 12 a Adamawa
<|section|>news
Gwamnatin jihar Adamawa a yau Lahadi ta tabbatar da barkewar cutar kwalara tare da hallaka mutane 12. Kwamishinan lafiya na jihar, Felix Tangwami, wanda ya tabbatar da ɓarkewar cutar a cikin wata sanarwa a Yola, ya ce daga cikin samfura 50 da ake zargin sun kamu da cutar, 30 sun kamu da cutar. Tangwami ya ce shida daga cikin wadanda suka mutu a asibiti ne, shida kuma a gida yayin da aka kwantar da kusan mutane 308 tare da 244 da aka yi musu magani kuma aka sallame su. “A madadin Gwamnan Jihar, ina so in sanar da ku duk cewa mun samu sakamakon samfurori da aka aika wa hukumar NCDC don tabbatarwa, an tabbatar da ɓarkewar Kwalara a jihar mu. “Abin takaici, daga cikin samfurori 50 da aka aika zuwa dakin gwaje-gwaje na Cibiyar Gwaje-gwajen Lafiya ta Ƙasa (NRL) da ke Abuja, samfurori 30 sun nuna akwai cutar kwalara, shida kuma sun nuna babu, biyu kuma ba a kammala ba, sannan 12 har yanzu sun makale.
|
34
|
<|title|>Ambaliya: Seyi Tinubu ya kai gudunmawar likitoci zuwa Maiduguri
<|section|>news
Seyi Tinubu, dan shugaban kasa, Bola Tinubu, ya kai gudunmawar ma’aikatan lafiya 50 domin bayar da tallafin jinya ga wadanda ibtila’in ambaliyar ruwa ya shafa a Maiduguri, Borno. Tinubu ya bayyana haka ne a wata ziyarar jaje da ya kai wa Gwamna Babagana Zulum, a jiya Juma’a a Maiduguri. Ya ce an tura ma’aikatan lafiya 50 da aka zabo daga jihohin Arewa-maso-Gabas don taimaka wa tawagar likitocin da aiki ya sha kansu a jihar. “Yanzu haka likitocin su nan sun fara wiki kuma za su kasance tare da ku na ‘yan kwanaki masu zuwa don taimakawa wajen shawo kan lamarin.” Tinubu ya ce tawagar tare da hadin gwiwar gidauniyar Noella sun ba da tallafin kayayyakin jinya da kuma kayan abinci da ba na abinci ba domin kula da yara da manya 50,000 da bala’in ya shafa. “Wannan somin-taɓi ne, Ina Mai tabbatar maka da cewa ƙarin taimako ya na nan tafe,” in ji Seyi.
|
35
|
<|title|>Sojoji sun kashe ƴan ta’adda 159 a mako guda – Shelkwatar tsaro
<|section|>news
Shelkwatar tsaro ta Nijeriya a jiya Juma’a ta ce sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 159 tare da kama 174 a mako daya da ya gabata. Daraktan yada labarai na shelkwatar tsaron, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a bayanan da ya fitar kan ayyukan rundunonin soji a Abuja. Edward Buba ya ce sojojin sun kuma ceto mutane 188 da aka yi garkuwa da su tare da kama masu shirya satar mai 45 da kuma kama makamai da alburusai. Ya ce, rundunar soji sun dauki matakai na kawo karshen ayyukan ta’addanci da matsalar tsaro a kasar nan. Acewarsa, ayyukan sojin suna haifar da sakamako mai kyau. “Bugu da kari, an tura karin sojoji don tabbatar da an gudanar da zaben jihar Edo ba tare da hargitsi ba. ” Rawar da sojoji ke takawa shi ne na bada goyan baya ga ‘yan sanda wajen kare masu zabe da kuma kawar da masu son tada hankali.” A Arewa maso gabas, Buba ya ce sojojin rundunar Hadin kai sun hallaka ‘yan ta’adda 41 tare da ceto mutane 48. Ya ce, ‘yan ta’adda 76 ne suka mika wuya ga sojoji tsakanin 11 ga watan Satumba zuwa 17 ga watan.
|
36
|
<|title|>NCC ta kwace jabun litattafai na kimanin Naira miliyan 5.7 a Enugu
<|section|>news
Hukumar Kare Hakkin Wallafa ta Ƙasa, NCC, ta kama wasu litattafai da aka kwaikwayon wallafa na sama da Naira miliyan 5.7 a wasu makarantu Enugu. Da ta ke jawabi yayin aikin kwace littattafan , Darakta a NCC, ofishin Enugu, Ngozi Okeke, ta ce aikin na daga cikin yunkurin hukumar na kawo karshen satar wallafa a Enugu. Ta jero sunayen littafan da ta kwace har da Ugo.C. Ugo- English and Mathematics series, New School Physics and Chemistry for Secondary Schools by Africana First Publishing Company da dai sauransu. Okeke ta ce an kwace litattafan daga kamfanonin buga littattafai daban-daban, wadanda aka jibge a cikin shagunan sayar da litattafai na makarantu da ke shirin sayar wa daliban. “Mun yi amfani da lokacin dawowa hutu, lokacin da masu satar wallafar ke sheke ayar su, mu kuma mu ke sa ido da binciken kwakwaf da kuma gudanar da ayyukan yaki da satar wallafa a wasu makarantun da ke sayen litattafai a wajen su. “Darajar litattafan da aka kwace sun kai Naira miliyan 5.7,” in ji ta. Okeke ta kuma bukaci jama’a da su marawa hukumar baya da sahihan bayanai da za su iya ba su damar magance matsalar satar wallafa a jihar.
|
37
|
<|title|>Zaɓen Edo: Ko nawa aka bani cin hanci ba zan karɓa ba – Kwamishiniyar INEC
<|section|>news
Farfesa Rhoda Gumus, kwamishiniyar zabe ta kasa dake lura da jihar Edo tayi alkawarin cewa baza ta karbi cin hanci da rashawa ba a zaben Gwamnan jihar dake gudana yanzu haka. Daily Trust ta rawaito cewa Gumus ta yi bayanin hakan ne a yayin tattaunawa da Channels TV. Ta sha alwashin cewa ba wanda ya isa ya tunkaret da maganar cin hanci saboda kimar ta. Kwamishiniyar zaben ta kara da cewa za a fara tantance masu zabe da karfe 8 inda ta ce ana sa ran kammala zaben da karfe 2 na rana amma duk wanda aka tantance za a bashi damar yin zaben. Tayi alkawarin cewa zaben na jihar Edo zai zama mafi inganci da INEC ta gudanar. Gamus ta ce, “Ni ce ke kula da Edo. Ina son yin abinda yake daidai duk da cewa bazan kasance a ko-ina ba. Zamu yi zaben nan cikin adalci. Bazan karbi toshiyar baki ba ko nawa ne. Ba sai na karbi Biliyoyin kudi zan yi abinda yake daidai ba. “Ba wanda ya isa ya gwada ni”, inji ta.
|
38
|
<|title|>Yadda Kwankwaso ya ɗauki nauyin yin magani ga yaron da ke fama da ciwon yunwa a Katsina
<|section|>news
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabi’u Musa Kwankwaso, ya dauki nauyin jinyar wani yaro mai suna Abubakar Ibrahim, dan shekara 13 da ke fama da cutar tamowa. Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa yaron dai mazaunin unguwar Yammawa ne, wani yanki a cikin birnin Katsina. Bidiyon yaron ta karaɗe shafukan sada zumunta, inda ya nuna yadda ya ke fama da ciwon tasowa kuma ya ke neman taimako. Daga nan ne sai shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Katsina, Armaya’u Abdulkadir, ya ce Kwankwaso ya ga bidiyon, kuma ya nuna damuwa kan halin da Ibrahim ke ciki. A cewar Abdulkadir, Kwankwaso ya nuna niyyar daukar nauyin jinyar yaron a ziyarar ta’aziyyar da ya kai ga iyalan Yar’adua bisa rasuwar mahaifiyar tsohon shugaban ƙasar. Ya kara da cewa “Kwankwaso ya bada umarnin a kai Ibrahim Kano domin samun kulawar da ta dace da sauran kulawar da ake bukata. “Nan da nan aka kai yaron asibitin Abdullahi Wase da ke unguwar Nasarawa a Kano, inda ya samu isassun magunguna da hankali da kuma samar da abinci da ake bukata da sauran sinadaran gina jiki. “Na gode wa Allah Madaukakin Sarki Ibrahim ya samu sauki, kuma an dawo da shi gida. Kamar yadda kake gani a yanzu, ya yi kyau kuma ya samu kumari. ” Iyayen yaron da sauran al’ummar unguwar sun godewa Kwankwaso bisa wannan taimako da ya yi.
|
39
|
<|title|>Karin farashin man fetur ya karya darajar mafi ƙarancin albashi na N70,000 — NLC
<|section|>news
Kungiyar kwadago ta Ƙasa, NLC, a jiya Alhamis ta ce za ta gana da gwamnatin tarayya kan yadda ma’aikata za su tsira daga karin farashin man fetur da aka yi a baya-bayan nan. A cewar kungiyar kwadago, farashin man fetur a halin yanzu ya durkusar da nasarorin da ake zaton an samu a kan sabon tsarin mafi karancin albashin ma’aikata na N70,000 da har yanzu ba a fara aiwatar da shi ba, in ji shugaban NLC, Joe Ajaero. Ya bayyana hakan ne a wajen bukin bude taron karawa juna sani na yini biyu kan aiwatar da mafi karancin albashi na shiyyar Kudu a Legas. Ya nanata cewa shugaban kasa Bola Tinubu ne ya yaudari kungiyar kwadago ta karbar mafi karancin albashi na N70,000 saboda ba zai yi karin farashin man fetur ba. Ya shawarci gwamnati da ta magance matsananciyar yunwa da fatara da bacin rai da ‘yan Najeriya ke fama da su kafin al’amura su kazance, yana mai korafin cewa lallai ‘yan Najeriya na cikin wahala.
|
40
|
<|title|>Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya na bana ba — Fadar shugaban kasa
<|section|>news
Shugaba Bola Tinubu ba zai halarci taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 79 a birnin New York na wannan shekara ba. Don haka, a wata sanarwa da Bayo Onanuga, mai baiwa shugaban kasa shawara na musamman, Tinubu ya umarci mataimakin sa, Kashim Shettima ya jagoranci tawagar Najeriya. Sanarwar ta ce shugaba Tinubu, wanda ya koma kasar a ranar Lahadin da ta gabata bayan tafiyarsa zuwa kasashen China da Birtaniya, yana son mayar da hankali kan al’amuran cikin gida da kuma magance wasu kalubalen da kasar ke fuskanta, musamman bayan da aka yi fama da bala’in ambaliyar ruwa. A taron Majalisar Dinkin Duniya 79, mataimakin shugaban kasa Shettima zai gabatar da bayanin kasa Najeriya ga babban taron, da halartar muhimman abubuwan da suka faru a gefe, da kuma gudanar da tarukan kasashen biyu. Babban Muhawara mai taken “Kada a bar kowa a baya: Yin aiki tare don ci gaban zaman lafiya, dauwamammen ci gaba da mutunta bil’adama na yanzu da na gaba” zai gudana ne daga ranar Talata 24 ga watan Satumba zuwa ranar Asabar 28 ga watan Satumba. 2024. (
|
41
|
<|title|>Bani da hannu a sabon yunkurin tsige Sarki Sanusi — Ganduje
<|section|>news
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta rade radin da ake yadawa cewa yana cikin yunkurin zargin da ake yi na tsige Muhammadu Sanusi na II daga matsayin Sarkin Kano. Leadership ta rawaito cewa Ganduje ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai taimaka masa kan fannin yada labarai da wayar da kan al’umma, Chief Oliver Okpala ya fitar. Shugaban na APC na mayar da martani ne kan wani rahoto dake yawo a shafukan sada zumunta mai taken “Ganduje na jagorantar sabon yunkuri na tsige Sarki Muhammad Sanusi a matsayin Sarkin Kano”. Rahotan ya ambato cewa “Majiyoyi daga fadar Kofar Kudu sun ce, Ganduje da wasu manyan mutane na yunkurin cire tsohon Gwamnan Bankin CBN a matsayin Sarkin Kano na 16 kuma shugaban majalisar Sarakunan Kano”. Sai dai a martanin da ya mayar Ganduje ya ce babu gaskiya a zargin, inda ya jaddada cewa bashi da hannu a yunkurin tsige Sarki Sanusi. Tsohon Gwamnan, ya ce shi yanzu ba Gwamna bane kuma ba shugaban majalisa ba don haka bashi da hannu kan tsigewa ko nada Sarki a Kano.
|
42
|
<|title|>Gwamnan Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi
<|section|>news
Gwamna Abba Yusuf na jihar Kano ya rushe shugabannin riko na kananan hukumomi 44 nan take. Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan, Sanusi Bature ya fitar. Rushewar tasu na zuwa ne, bayan majalisar dokokin jihar Kano ta kara musu wa’adi zuwa watanni 2, inda wa’adinsu ya kare a ranar 8 ga watan Satumba. Karin lokacin, acewar ‘yan majalisar an yi shi ne don tabbatar da dorawa a shugabancin karamar hukuma. An shirya gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar Kano dai ranar 26 ga watan Oktoba. Abba Yusuf ya umarci tsoffin shugabannin na riko da su mika ragamar jagorancin kananan hukumomin ga daraktocin mulki. “Wannan rushewar ta shafi dukkan shugabanni da mataimakansu da Sakatarori da Kansiloli”, inji Gwamnan. Ya bayyana godiya ga shugabannin na riko bisa gudunmawar ra suka bayar wajen ci gaban yankunan su tare da alkawarin yin aiki tare anan gaba.
|
43
|
<|title|>Gwamnatin Kano za ta gina gidaje kyauta ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa
<|section|>news
Gwamnatin jihar Kano ta yi alkawarin gina gidaje kyauta ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a fadin kananan hukumomi 44 na jihar. A wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamna jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce za a yi hakan ne don rage radadin da ambaliyar ta haifar a jihar. Dawakin Tofa ya ce, Gwamna Abba Kabir Yusuf ne ya bayyana hakan a yayin zaman majalisar zartarwa da ya gudana a fadar gwamnatin Kano a jiya Laraba. Ya ambato Gwamnan na bayanin cewa gidajen da za a samar za taimakawa wadanda ambaliyar ruwa ta shafa wajen samun matsuguni ga iyalansu. Ya ce, gwamnatin jihar na hada gwiwa da ma’aikatar jinkai da yaki da talauci domin taimakawa mutanen da kayan abinci da abubuwan rayuwa na yau da kullum. Gwamnan ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar na shirin raba kujeru da ababen zama a mataki na farko ga daliban makarantun firamare da Sakandare 220, 000 domin inganta fannin koyo da koyarwa. Gwamna Yusuf, ya ce bisa ayyana dokar tabaci a fannin ilimi a jihar, gwamnatin zata raba kayan makaranta na sawa ga dukkan daliban ajin farko na makarantun firamare.
|
44
|
<|title|>Mai-ɗakin Shugaban Ƙasa, Remi Tinubu ta bada tallafin miliiyan 500 ga wadanda ambaliya ta shafa a Maiduguri
<|section|>news
Uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu ta bada tallafin Naira Miliyan 500 ga mutanen da ambaliyar ruwa ta shafa a birnin Maiduguri na jihar Borno. Oluremi ta sanar da bada tallafin ne a ziyarar jaje da ta kai ga Gwamna Babagana Zulum a jiya Laraba a birnin Maiduguri. Matar shugaban kasar, wacce ta samu wakilcin matar mataimakin shugaban kasa, Nana Kashim Shettima wacce ta gabatar da tallafin ta Naira Miliyan 500 ga wadanda abin ya shafa. Ta yabawa gwamnatin jihar bisa kokarin ta a kowanne mataki. Da yake jawabi, Gwamna Zulum ya yaba da tallafin, inda ya kara da cewa shirin RHI ya tallafawa mata da dama da masu karamin karfi a jihar. Ya ce, shima shugaban kasa Tinubu ya ziyarci Maiduguri a ranar Litinin domin jajantawa al’ummar jihar kan iftila’in.
|
45
|
<|title|>DA ƊUMI-ƊUMI: Gobe NECO za ta saki sakamakon jarrabawar 2024
<|section|>news
Hukumar Shirya Jarrabawar Kammala Makarantun Sakandare ta Ƙasa, NECO za ta saki sakamakon jarrabawar 2024 a gobe Alhamis. Wata majiya mai tushe a hukumar ta shaidawa jaridar DAILY NIGERIAN HAUSA cewa, hukumar ta kammala shirin sakin sakamakon jarrabawar a gobe. Acewar majiyar, Rijistaran hukumar ne ake sa ran zai sanar da sakamakon da misalin karfe 12 na rana. Dalibai dai sun zana jarrabawar ne a watan Yuni da Yuli na shekarar da muke ciki.
|
46
|
<|title|>Kotu ta ɗage ranar hukunci kan ƙarar da aka shigar don sauke Ganduje a matsayin shugaban APC
<|section|>news
A yau Laraba ne wata babbar kotun tarayya da ke Abuja ta dage yanke hukunci a karar da ta shigar da ke neman tsige Dr Abdullahi Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa zuwa ranar 23 ga watan Satumba. Zaman hukuncin, wanda tun da farko aka saka za a yi shi a yau, ba ya cikin jerin kararrakkn da aka ambata a yau. NAN ta tattaro cewa tun da fari, magatakardar kotun ya tuntubi masu kara da wadanda ake kara domin a dage ranar da za a yanke hukunci saboda hukuncin bai kammala ba. “Mun kira bangarorin biyu ta wayar tarho domin sanar da su halin da ake ciki. Sabon kwanan wata shine mako mai zuwa, Satumba 23, ”in ji wata majiya mai tushe. Tun a ranar 5 ga watan Yuli, Mai Shari’a Inyang Ekwo ya sanya yau a matsayin ranar yanke hukunci. Masu shigar da karar sun bukaci kotun da ta hana Ganduje ci gaba da bayyana kansa a matsayin shugaban jam’iyyar APC. Mai kara; Kungiyar APC ta Arewa ta Tsakiya, karkashin jagorancin Saleh Zazzaga ce ta shigar da karar ne domin neman bahasi kan halascin nadin Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC alhalin shi ba dan shiyyar Arewa ta tsakiya ba ne. A cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/599/2024, mai shigar da karar ya bayyana Ganduje da APC da kuma hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC a matsayin wadanda ake kara na 1 zuwa 3.
|
47
|
<|title|>RAGE MUGUN IRI: An kama masu baiwa ƴan fashin daji bayanan sirri su 1,000 a Katsina – Gwamna Radda
<|section|>news
Gwamnan jihar Katsina, Umaru Dikko Radda ya baiyana cewa ƴan banga na CWC da ke aikin samar da tsaro a jihar sun kama mutane 1, 000 da ke aikin kaiwa ƴan fashin daji bayanai. Acewar Gwamnan, nasarar na daga cikin kokarin gwamnatin jihar na tabbatar da tsaro da kuma ganin an bunkasa fannin noma a jihar. Jaridar LEADERSHIP ta rawaito cewa gwamnan ya bayyana hakan ne a yayin ziyarar da Babban Hafsan Sojin Sama, Hassan Abubakar ya kai masa inda ya bayyana alfanun alaka tsakanin rundunar sojin sama da gwamnatin jihar wajen magance ayyukan ‘yan fashin daji. Ya tabbatar wa rundunar sojin goyan bayan jihar a kokarin da ake yi ta kowacce fuska. Gwamna Radda ya bayyana nasarorin da aka samu da yadda aka kama masu baiwa ‘yan ta’adda bayanai. Ya kuma ce gwamnati ta gana da masu ruwa da tsaki a kananan hukumomin jihar don kawar da ‘yan ta’adda. Bugu da kari, Gwamnan ya ce rashin aikin yi da jahilci da matsin rayuwa na daga cikin abubuwan dake haifar da matsalar tsaro a jihar.
|
48
|
<|title|>Ambaliya: Tinubu ya sauka a Maiduguri domin ziyarar jaje
<|section|>news
Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauka a birnin Maiduguri na jihar Borno domin jajanta wa al’ummar jihar bisa ibtila’in ambaliyar ruwa da ta samu garin. A jiya ne dai Tinubu ya dawo daga tafiya, inda ya je China da Burtaniya. Tun ya na can ya umurci mataimakin sa Kashim Shettima da ya ziyarci Maiduguri ya ga abinda ke faruwa. Sai shi ma Shugaban ya tashi kafa da kafa zuwa Maiduguri, inda ya sauka da misalin ƙarfe 3:20 na rana.
|
49
|
<|title|>Mun kwashi shekaru mu na yi wa Kwankwasiyya hidima amma ba a baiwa ko mutum ɗaya takara a cikin mu ba — R-APC
<|section|>news
Ƴan ƙngiyar magoya bayan jam’iyyar NNPP Kwankwasiyya, da su ka yi mata laƙabi da R-APC sun koka kan yadda jam’iyyar ta fitar da ƴan takara a zaben kananan hukumomi mai zuwa a Kano ba tare da an baiwa ko mutum ɗaya daga cikin su takara ba. R-APC, wacce aka kafa tun 2018, na daya daga cikin ƙungiyoyin da ke nuna goyon baya ga tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, shugaban darikar Kwankwasiyya tun ya na jam’iyar APC a daidai lokacin da aka rigimar sa da Abdullahi Umar Ganduje ta yi ƙamari. A yayin zantawa da Daily Nigerian Hausa, Ciyaman din R-APC, Sa’idu Yahaya Adam, ya bayyana mamakinsa kan tsarin da jam’iyyar NNPP ta bi wajen fitar da ‘yan takarar. “Abin al’ajabi ne tattare dani mussaman a wannan jiha tamu mai albarka, a karkashin wannan ƙungiya ta R-APC Kano state mu ka yi al’ajabin abinda ya faru a fitar da ƴan takara da aka yi nasa Kansiloli a wannan jiha ta mu. ” Mun tashi da alhini da takaici halin da muka tsinci kanmu”, inji shi. Sa’idu Yahaya, ya ce a baya jagorori sun yi musu alkawarin cewa ba yadda za a yi su wulakanta sai dai ba a sanya musu ko mutum daya ba a cikin ‘yan takara na kansila. Kungiyar wacce ta ce tun 2018 suke kan tsarin Kwankwasiyya sun roki jagoran NNPP na kasa, Sanata Rabiu Kwankwaso ya sanya baki kan abinda aka yi musu. A makon da ya gabata ne dai jam’iyyar NNPP ta fitar da ‘yan takara a zaben shugabannin kananan hukumomi da Kansiloli da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai kamawa a jihar Kano. Sai dai a wata hira da ya yi da Freedom Radio, shugaban NNPP na jiha, Hashimu Dungurawa ya ce duk wanda ya ke da korafi ya rubuto kuma idan aka duba aka ga ƙorafin nasa a kan gaskiya ya ke to za a bi masa hakkin sa.
|
50
|
<|title|>Ƴan bindiga sun kashe mutanen da su ka sace tare da waɗanda su ka je kai kuɗin fansa a Neja
<|section|>news
Waɗanda su ka yi garkuwa da wani mamallakin otel da manajan sa da wasu baƙi a garin Gauraka da ke ƙaramar hukumar Tafa a jihar Neja sun kashe su bayan karɓar kuɗin fansa na Naira Miliyan 25. Daily Trust ta ce rahotanni sun bayyana cewa ƴan fashin dajin sun kuma kashe mutane biyu da su ka kai kuɗin fansar. Tsohon shugaban ƙaramar hukumar Tafa, wanda ɗan uwa ne ga daya daga cikin waɗanda aka kashe, Yau Ahmad, ya ce an kashe mutanen ne a dajin Dogon -Daji wanda ke iyakar Kaduna da Neja da birnin tarayya Abuja. Ya ce an kai gawarwakin mutanen zuwa ofishin rundunar sojan-sama da ke kusa da filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe a Abuja bayan gano gawarwakin a dajin. Kwamandan ƴan bijilanti a karamar hukumar Tafa, Hussaini Abubakar ya ce an binne gawar mutane biyu da suka kai kuɗin fansa waɗanda mambobin su ne bayan amincewar sojoji. Jaridar Daily Trust ta rawaito yadda aka sace mutanen a ranar 17 ga watan Agusta. Wani mazaunin garin ya ce maharan sun kai farmaki da karfe 1 na dare otel din inda su ka sace duk baƙin da su ka kama ɗaki.
|
51
|
<|title|>Gwamnatin Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ta shafa a Maiduguri
<|section|>news
Gwamnatin jihar Kano ta bada tallafin Naira Miliyan 100 ga wadanda ambaliyar ruwa ya shafa a jihar Borno. Kamfanin dillancin labarai na NAN ya rawaito cewa kwamishinan yada labarai, Baba Halilu Dantiye ne ya mika cak na kudin tare da kwamishiniyar jinkai, Amina Sani a madadin Gwamna Abba Kabir Yusuf. Gwamna Babagana Zulum ne ya karbi wakilan gwamnan a gidan gwamnatin jihar Borno. Abba Yusuf, ya jajantawa wadanda abin ya shafa inda ya bayyana amabliyar a matsayin babban bala’i. Yayi kira da a kara tallafawa mutanen da kuma bayani kan alfanun hada karfi da karfe wajen magance irin wannan ambaliyar. Abba Kabir Yusuf ya kuma jaddada goyan bayan jihar Kano ga al’ummar Borno a wannan yanayi da suke ciki. Gwamnan ya kuma yi addu’a ga wadanda suka rasa ransu da addu’ar neman sauki ga wadanda suka jikkata. Anasa jawabin, Gwamna Zulum ya godewa Gwamnatin jihar Kano bisa tallafin da ta basu.
|
52
|
<|title|>NNPC ya fitar da farashin man fetur da ya saro daga matatar man Dangote
<|section|>news
Kamfanin mai na kasa, NNPCL ya fitar da kiyasin farashin litar man fetur da ya saro daga matatar mai ta Dangote, bisa farashin watan Satumba, 2024. Kamfanin NNPC ya bayyana cewa, bisa ga tanadin dokar masana’antar man fetur (PIA), ba gwamnati ce za ta kayyade farashin man fetur ba, sai dai ta na yarjejeniya ne kai tsaye tsakanin ta bangarorin kan tsayar da farashin. NNPC ya ce ya tabbatar da cewa ya saro man daga matatar man Dangote da dalar Amurka a watan Satumba, saboda ciniki da Naira zai fara ne daga ranar 1 ga Oktoba, 2024. Kamfanin na NNPC ya bayar da tabbacin cewa idan farashin ya yi tsada, za ta yi godiya ga duk wani rangwamen da matatar Dangote za ta yi, shi kuma zai sayarwa jama’a a hakan ba tare da ƙari ba. Ga yadda farashin man zai kasance a gidajen man fetur na NNPC a ƙasar nan, bisa farashin watan Satumba na 2024. Sokoto: N999.22 Kano: N999.22 Kaduna: N999.22 Abuja: N992.22 Borno: N1,019.22 Oyo: N960.22 Imo: N980.22 Rivers: N980.22 Lagos: N950.22
|
53
|
<|title|>Tinubu ya taya al’ummar Musulmi murnar Maulidin Ma’aiki
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Tinubu ya aika da sakon taya murna da fatan alkhairi ga al’ummar Musulman Nijeriya a ya yin da ake bikin murnar Maulidin Annabi MUHAMMAD (S.A.W) Shugaban kasar ya yi kira ga Musulmai da su yi amfani da lokacin wajen koyi da halayen Fiyayyen Halitta. Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwar da mai taimakawa shugaban kasar kan fannin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar a yau Lahadi. “A yayin da muke bikin Maulidi, yakamata mu yi koyi da rayuwar Annabi Muhammad S.A. W da dabi’un sa na tausayi da jin kai”, dole ne mu yi koyi da wadannan halaye na kwarai”, inji shi. Shugaban kasa Tinubu ya kuma yi kira ga al’ummar Musulmi da su yi amfani da lokacin hutun Maulidin wajen yiwa kasa addu’a da nuna kauna da jin kai ga kowa.
|
54
|
<|title|>Matsin rayuwa: Mafi yawan farfesoshi a talauce su ke — Farfesa Audi
<|section|>news
Farfesa Audi T. Giwa, shugaban tsangayar sashen ilimi da ba na kimiyya a jami’ar jihar Kaduna (KASU), ya bayyana cewa yawancin farfesoshi a Najeriya na fama da talauci. Ya kara da cewa, a halin yanzu, farfesoshi kadan ne ke iya tuka mota saboda rashin wadataccen albashi da kuma matsalolin tattalin arziki. Audi ya bayyana hakan ne biyo bayan gabatar da wata maƙala a wani taro da kungiyar ‘Pharmafluence Education Advancement Network (PEAN)’ ta shirya tare da hadin gwiwar jami’ar jihar Kaduna. Ya ce galibin farfesoshi a Najeriya na ɗaukar albashi kasa da Naira dubu 500 duk wata, amma duk da haka al’umma na kallon su a matsayin masu kudi. “Mutane nawa kuka sani yanzu wadanda ba za su iya tuka motocinsu ba? Wadannan mutane ne masu arziki; su ba farfesoshi bane, domin mun riga mun talauce. Idan ka ga farfesa yana tuka mota, to suna cikin ƴan kaɗan. Amma duk da haka al’umma na kallonmu a matsayin manyan mutane,” inji shi. “A ce ni ne na fada a ko’ina—babu wani farfesa a kasar nan da ya ke karbar sama da Naira 500,000 a wata. Wasu suna samun kusan N300,000. Duk da wannan, mutane suna kallon mu a matsayin masu kudi. Idan ku ka ce ba ku da kuɗi, sai su bata rai, wannan ita ce gaskiyar,” in ji shi
|
55
|
<|title|>Mutane 4 sun rasu kuma 36 na kwance a asibiti sakamakon ɓarkewae cutar kwalara a Yola
<|section|>news
An samu barkewar cutar kwalara a karamar hukumar Yola-ta-Arewa a jihar Adamawa, wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane hudu tare da kwantar da mutane 36 a asibiti, a cewar Jibrin Ibrahim, shugaban ƙaramar hukumar. Ibrahim ya bayyana hakan ne ga manema labarai yayin wata ziyara da ya kai wa wadanda lamarin ya shafa a cibiyar yaki da cututtuka masu yaduwa (IDC) da ke Yola, a yau Lahadi. Ya bayyana cewa cutar ta barke ne a unguwannin Alkalawa, Ajiya, da Limawa da ke cikin ƙaramar hukumar. Bayan isowarsa, Ibrahim ya ba da rahoton cewa an fara samun mutane 20 da suka kamu da cutar, amma adadin ya karu da sauri zuwa 40, yayin da hudu su ka rasu. Ya yi nuni da cewa an kwantar da marasa lafiya da dama kuma suna samun kulawar likitoci daga ma’aikatan lafiya. Shugaban ya kuma yaba da saurin martanin da ma’aikatan lafiya, Red Cross, da abokan hulda na kasa da kasa suka bayar wajen magance barkewar cutar.
|
56
|
<|title|>Sabon shugaban NAHCON ya kama aiki yayin da ya yi ganawar farko da jami’an hukumar
<|section|>news
Farfesa Abdullahi Saleh, shugaban riƙo Hukumar Alhazai ta Ƙasa, NAHCON, ya yi zaman farko da jami’an hukumar tun bayan naɗa shi da shugaba Bola Tinubu ya yi a kwanan nan. Farfesa Saleh ya yi taron ne a ranar Juma’a, wanda ya samu halartar jiga-jigan jami’an hukumar. A jawabinsa na bude taron, shugaban ya mika godiyarsa ga Ubangiji da ya ba shi damar yi wa ƙasa hidima. Ya kuma lura da damuwa cewa daga cikin bayanan tarukan da su ka gabata a baya, akwai batutuwan da su ka dace da ke bukatar tattaunawa ta gaggawa a kansu. Farfesa Saleh ya kuma yi addu’ar Allah ya ba sa a yi tattaunawa mai amfani da albarka. Taron ya samu halartar Kwamishinan Tsare-tsare, Bincike, Kididdiga, Labarai da Ayyukan Ma’ajiyar Kundaye (PRISLS) Farfesa Abubakar A. Yagawal, Kwamishinan Ayyuka, Gani da Ido da Lasisi, Prince Anofi Elegushi (OIL) ) da Kwamishinan Manufofi, Kula da harkokin ma’aikata da Harkokin kudi (PPMF) Prince Aliu AbdulRazaq. Dr Saleh Usman Muhammad, Mataimakin Shugaban riko na musamman (Bangaren Dabaru).
|
57
|
<|title|>Yakamata a riƙa baiwa mata rol iri daban-daban kamar maza a fim — Jaruma Kanyin Eros
<|section|>news
Jarumar fim Kanyin Eros ta ce ya kamata a rika baiwa mata rol masu wuya kuma iri daban-daban kamar yadda a ke bawa maza a fina-finai. Da ta ke magana da mujallar Sunday Scoop, ta ce, “Mata na iya zama komai. Su na iya buga rol din mugunta, jarumai, masu binciken laifuka. Duk wata rawar da za a iya ba wa maza kuma za a iya ba wa mata. Mu ma za mu iya yi.” Ta bayyana cewa ya kamata masana’antar ta kasance a buɗe kofa ga mata da yawa su rika hawa rol daban-daban fiye da irin wanda aka saba basu na iyaye, kwalliya da sauransu. “Masana’antar tana da wahala. Akwai mata masu hazaka da yawa a wajen, amma bana jin akwai isassun ayyuka da ake basu,” inji ta.
|
58
|
<|title|>An kama mutane 4 kan zargin kashe dalibar jami’a a Kogi
<|section|>news
Yansanda sun kama mutane 4 da ake zargi da hannu a kisan wata dalibar jami’ar tarayya da ke Lokoja, jihar Kogi. Ana zargin wani matashi da sace dalibar mai shekaru 17 da ke aji na farko a jami’ar, inda kuma ya kashe ta. Mai magana da yawun rundunar ƴansanda a jihar, SP Williams Ovye-Aya, ne ya sanar da hakan yayin ganawa da manema labarai. Onye-Aya ya ce babban wanda ake zargin ya hada kai da abokanan sa uku wajen aikata laifin. “Jami’an ‘yan sandan Nijeriya dake sashin binciken manyan laifuka a jihar Kogi, sun kama Jeremiah Paul-Awe na karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna a ranar 11 ga watan Satumba. ” Paul shi ne ya sace dalibar kuma ya kashe ta. “Mun karbi korafi daga Stephen Oluwoyo cewa ‘yar sa ta bata kuma baya samun ta. ” Mahaifin nata ya kara da cewa ya samu sakon waya daga wata sabuwar lamba cewa an yi garkuwa da ‘yar sa kuma ana neman kudin fansa”, inji shi. Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda ake zargin sun amsa laifin su. Sannan za a gurfanar dasu gaban kotu da zarar an kammala bincike.
|
59
|
<|title|>2027: Bana shirin zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa — Obi
<|section|>news
Dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar Labour Party a zaben 2027, Peter Obi, ya ce bashi da sha’awar zama dan takarar mataimakin shugaban kasa ga kowa a zaben 2027. Daily Trust ta rawaito cewa Obi ya bayyana hakan ne a yau Asabar a shafin sa na X. Acewarsa, an yi wa wasu kalamai da ya yi yayin ganawa da News Central TV gurguwar fahimta. Obi ya ce a yayin tattaunawar, ya yi amfani da damar wajen yin bayani kan matsayar sa dalla-dalla, amma wasu mutanen suka dinga yada akasin hakan. “Domin kaucewa rudani, ni ban ce zan zama mataimakin shugaban kasa ba”. ” Na sha fada cewa, a shirye nake nayi aiki da wadanda ke son gina sabuwar Nijeriya. “Bana son zama irin mutanen dake ta babatu kan batun 2027 a yayin da ‘yan Nijeriya ke fama da yunwa da matsalar tsaro da sauran kalubale”, inji Obi.
|
60
|
<|title|>Matsalar tsaro da ambaliyar tasa manoma 46, 000 rasa muhallin su a Niger
<|section|>news
Jimillar manoma 46, 853 daga gidaje 5, 863 ne suka rasa muhallansu sakamakon ayyukan yan fashin daji da ta’addanci da ambaliyar ruwa da rikicin makiyaya da manoma a fadin jihar Niger. Wani rahota da hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Niger ta samu ya nuna cewa wasu daga cikin manoman sun rasa muhallinsu sakamakon ayyukan ‘yan fashin daji tun 2018. Bayanan sun nuna cewa manoman da abin ya shafa sun hada da maza 5, 863 da mata 23, 450 da kananan yara 17, 740. Hukumar ta ce akwai ‘yan gudun Hijrah 5, 823 a sansanin ‘yan gudun Hijrah na Gwada da ya hada da maza 970 da mata 2, 051 da kananan yara 2, 802. A sansanin ‘yan gudun Hijrah na Kuta, hukumar NSEMA ta bayyana cewa akwai manoma ‘yan gudun Hijrah 3, 180 wadanda ya hada maza 530 da mata 1, 040 da kananan yara 1, 610 inda ta ce an bude dukka sansanonin a 2018.
|
61
|
<|title|>Ambaliya: Na damu matuka kan yiwuwar samun ƴan Boko Haram da su ka tsere daga kurkuku — Zulum
<|section|>news
Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Umara Zulum, ya ce ya shiga damuwa kan yiwuwar wasu kwamandojin Boko Haram sun tsere daga gidan gyaran hali na jihar sakamakon ambaliyar ruwa da ta afkawa garin Maiduguri. Ambaliyar ruwan dai ta jawo asarar rayuka da dukiyoyi a jihar. Acewar rahotanni, ambaliyar ruwan ta lalata wani bangare na tsohon gidan bursin inda aka debe daurarru da dama zuwa sabon gidan bursin matsakaici a Maiduguri. Wata majiyar tsaro ta tabbatar da hakan ga wakilin Daily Trust. Wasu rahotanni da ba a tabbatar ba, sun ce yayin da aka kwashe wasu daga gidan kurkukun, wasu kuwa sun tsere. Yayin da aka tambaye shi, ko yana damuwa kan cewa wasu shugabannin Boko Haram ka iya tserewa, sai Gwamnan Zulum ya mayar da amsa da cewa ya damu. Ya ce, “Ina damuwa, eh, ina damuwa matuka. Amma ya kamata kasa a ran ka cewa gwamnatin jihar Borno ta kafa inda ‘yan tada kayar baya zasu tuba. Shekaru 2 da suka gabata, Mayakan Boko Haram da iyalansa 200, 000 suka tuba, kuma ina tunanin hakan yana haifar da sakamako mai kyau wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya da kwanciyar hankali” Zulum ya kuma koka kan yadda jihar ta sake samun kanta cikin annoba a yayin da take fuskantar matsalar tsaro. “Zan iya tunawa, an kashe sama da mutane dubu 300, an lalata dubban ajujuwa na karatu, ‘yan tada kayar baya sun lalata daruruwan wurare. ” Muna ta kokarin fita daga wannan matsalar, yanzu kuma ga wani bala’in”.
|
62
|
<|title|>Maulidi: Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin a matsayin ranar hutu
<|section|>news
Gwamnatin tarayya ta ayyana Litinin 16 ga watan Satumba a matsayin ranar hutu domin bikin murnar haihuwar Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallama. Bayanin hakan na dauke ne cikin wata sanarwa da babban Sakatare a ma’aikatar harkokin cikin gida, Dakta Magdalene Ajani ya fitar a ranar Juma’a. Ajani, yayi bayanin cewa, ministan harkokin cikin gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo ne ya sanar da hutun a madadin gwamnatin tarayya, inda ya taya al’ummar Musulmi murna. Tunji-Ojo ya bukaci al’ummar Musulmi da ‘yan Nijeriya da su yi koyi da halayen hakuri da sadaukar da kai. Yayin da yake taya al’ummar Musulmi murna, ministan ya nemi al’ummar Musulmi da su yi amfani da damar wajen yiwa kasa addu’ar samun zaman lafiya.
|
63
|
<|title|>Sojoji sun hallaka rikakken ɗan ta’adda, Halilu Sububu da mayakan sa a Zamfara
<|section|>news
Rahotanni daga jihar Zamfara na nuni da cewa sojojin Najeriya sun hallaka Halilu Sububu, dan ta’adda da ya yi kaurin suna a yankin Arewa maso Yamma. Sububu, wanda ya kwashe shekaru ya na ta’addanci a jihar Zamfara, ya gamu da ajalin sa a jiya Alhamis. Wata majiyar asiri ta tsaro a safiyar yau Juma’a ta tabbatar da kisan dan ta’addan da sojoji su ka ga jaridar PRNigeria. “A wani samame da dakarun soji suka kai jiya, sun yi nasarar hallaka shahararren dan bindigar nan Halilu Sububu tare da wasu ‘yan bindiga da dama a Zamfara a daren jiya. “Sojoji sun kuma kwato muggan bindigogi da alburusai, tare da babura daga hannun ‘yan ta’adda,” in ji majiyar.
|
64
|
<|title|>YANZU-YANZU: PDP ta dakatar da Dino Melaye
<|section|>news
Jam’iyyar PDP ta dakatar da Sanata Dino Melaye daga jihar Kogi kan wasu zarge-zarge na yi wa jam’iyyar zagon-ƙasa. Wannan mataki , a cewar wata takarda da jaridar TRIBUNE ONLINE ta gani a yau Juma’a, kwamitin gudanarwar jam’iyyar na gundumar Ayetoro/Iluagba Ward 1 ya yanke shi ne bayan nazarin rahoton kwamitin ladabtarwa da aka kafa domin bincikar laifukan da Melaye ya aikata. Ga dukkan alamu abubuwan da Melaye ya yi a baya-bayan nan sun saɓawa wa manufofin jam’iyyar PDP da hadin kai, wanda ya sa aka dakatar da shi.
|
65
|
<|title|>Tinubu ya bai wa jihohi Naira biliyan 108 don magance ambaliya da zaizayar ƙasa – Shettima
<|section|>news
Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya amince da kuɗi Naira biliyan 108 ga jihohi 36 na ƙasar domin yaƙi da ambaliya da sauran nau’ukan bala’o’i. BBC Hausa ta rawaito cewa Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima ne ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Fadar Shugaban Ƙasa a ranar Laraba. Da yake bayyani a lokacin da ya karɓi baƙuncin Shugaban Majalisar Wakilan Najeriya, Abbas Tajudden, ya bayyana ambaliyar ta Borno a matsayin “bala’i ga ƙasar baki ɗaya.” “Shugaba ƙasar ya nuna niyyarsa ta haɗa hannu da jihohi domin magance irin waɗannan matsalolin,” inji Shettima. “Ba a daɗe ba ya amince a ba kowace jiha Naira biliyan uku domin magance irin waɗannan matsalolin,” kamar yadda shafin talabijin na Channels na intanet ya ruwaito. A nasa ɓangaren, Tajudeen ya jajanta wa Shettima da Tinubu da gwamnati da al’ummar Borno bisa wannan ibtila’in, sannan ya tabbatar da cewa majalisa za ta taimaka wa waɗanda lamarin ya shafa. “In sha Allah komai zai wuce kuma mutane za su koma garuruwansu, su cigaba da rayuwarsu kamar yadda suka saba kamar babu abun da ya faru. Don Allah ka isar mana da saƙonmu na jaje zuwa ga gwamna da al’ummar Borno,” inji shi.
|
66
|
<|title|>Har yanzu farashin man fetur bai kai matakin da ya kamata ya kai ba a Nijeriya — IMF
<|section|>news
Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ya ce har yanzu ba a kai farashin man fetur ɗin asalin farashinsa na kasuwa ba a Nijeriya. Hakan na nuni da cewa za a iya ƙara farashin a nan gaba kamar yadda jaridar Vanguard ta rawaito ta bakin Babban wakilin IMF a Najeriya, Dokta Christian Ebeke a yayi da yake jawabi a tattaunawarsa da gidan talabijin na Arise TV a jiya Alhamis. Sai dai kuma adaidai lokacin da ake ci gaba da muhawara a kan ƙarin farashin man fetur, Asusun Lamuni na Duniya, IMF, ya buƙaci gwamnatin Najeriya da ta ba ɓangaren rage wa talakawan ƙasar raɗaɗi muhimmanci. Babban jami’in na IMF ya bayyana damuwarsa a kan irin wahalar da ƴan Najeriya suke ciki a sanadiyar wasu matakai da gwamnatin ƙasar ta ɗauka. A cewar Ebeke, “Ina tunanin ƙarin farashin man ya zo ne a daidai lokacin da ƴan Najeriya suke cikin tsananin rayuwa. “Ƴan Najeriya suna fama da matsaloli da dama kamar hauhawar farashin kayayyaki kamar su abinci ga ambaliya da sauransu. “Don haka ƙara farashin man sai ya zo a daidai lokacin da tattalin arzikin ƙasar ke tangal-tangal, kuma ƴan Najeriya ke cikin tsananin rayuwa.”
|
67
|
<|title|>Hajjin 2025: Hukumar alhazai ta Adamawa ta buƙaci maniyyata su fara ajiye Naira miliyan 8.2
<|section|>news
Shugaban Hukumar Jin dadin Alhazai ta jihar Adamawa, Malam Abubakar Salihu ya kira wani taron gaggawa da jami’an aikin hajji na kananan hukumomi a jihar. A wata sanarwa da sashen yaɗa labarai na hukumar ya aikewa Hajji Reporters Hausa, Salihu ya kira taron ne kan tsare-tsaren jadawalin shirye-shiryen aikin Hajjin badi. A yayin ganawar, Malam Salihu ya yi jawabi a kan batutuwa da dama, inda mafi fice a cikin su shine kudin aikin Hajjin 2025. A cewar sanarwar, shugaban hukumar ya yi kira ga maniyyata daga jihar da su je banki su fara ajiye Naira miliyan 8.2 na kudin aikin Hajjin kafin hukumar alhazai ta ƙasa ta yanke cikakken farashin aikin hajji na shekara mai zuwa. Ya kuma umarci jami’an hajji da su fara aikin rijistar maniyyata a kananan hukumomin da su ke aiki.
|
68
|
<|title|>Halin da Nijeriya ta faɗa a hannun Tinubu na damun mu — Ciyamonin APC na jihoh
<|section|>news
Shugabannin jam’iyyar APC mai mulki a jihohi 36 na tarayya da kuma Abuja sun yanke shawarar ganawa da kwamitin koli na jam’iyyar (NWC) da kuma shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan halin da ƙasar nan ta shiga. Daily Trust ta rawaito cewa sakataren kungiyar shugabannin jam’iyyar APC na jihohi kuma shugaban ta a jihar Cross River, Alphonsus Ogar Eba ne ya bayyana hakan ga manema labarai a yau Alhamis bayan taron da su ka yi a Abuja. Ogar, wanda ke tare da shugaban riko na kungiyar, Honarabul Cornelius Ojelabi, da sauran shugabannin jihohi ya ce taron zai tattauna batutuwa da dama da gwamnatin tarayya ciki har da na kuncin rayuwa a kasar. Ya ci gaba da cewa, “A jiya ne kungiyar shugabannin jam’iyyar APC ta Jihohi su ka yi taro domin tattauna batutuwan da su ka shafi tsarin dimokuradiyyar jam’iyyar da kuma nasarar gwamnatinmu ta APC a karkashin ingantaccen jagorancin Shugaba Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa, Sanata. Kashim Shettima GCON Da ya ke amsa tambayoyi daga manema labarai kan wahalhalun da kasar ke ciki a yanzu, Ogar ya ce, “Game da kuncin rayuwa, eh, kowa na da korafi. Mu na sane da hakan kuma shi ne mu ka ce za mu yi ganawar sirri da NWC da gwamnati. “Don haka gwamnatin da muke nufi ita ce gwamnatin tarayya. Har sai an yi faxa da tsifa naga sakamako, amma yanzu ya yi wuri a yi magana da manema labarai kan wadannan batutuwa.”
|
69
|
<|title|>Za mu shiga zaɓen ƙananan hukumomi a Kano — APC
<|section|>news
Jam’iyyar APC a jihar Kano tace za ta shiga zaɓen ƙananan hukumomi da za a gudanar a ranar 26 ga watan Oktoba mai zuwa. A sanarwar da kakakin jam’iyyar, Hon. Ahmad S Aruwa ya fitar yace bayan karbar rahoton kwamitin da ya tattara shawararwari don shiga zaben, jam’iyyar ta yanke hukunci shiga a matsayinta Na jam’iyya mai mulki a Najeriya. Sanarwar ta kuma umarci dukkanin masu sha’awar takarar su kai takardar nuna sha’awa ga ofishin jam’iyyar dake kananan hukumomi tun daga ranar 12 zuwa 14 ga watan Satumba. Idan za’a iya tunawa a kwanakin baya jam’iyyar APC ta jihar kano ta kafa wani kwamiti karkashin jagorancin Rabi’u Sulaiman Bichi, domin su duba yiwuwa jam’iyyar ta shiga zaben ko kar ta shiga. Daga karshe dai a jiya laraba kwamiti ya mika rahotonsa, kuma ga shi a yau jam’iyyar ta amince zata shiga a fafata da ita a zaɓen shugabannin kananan hukumomin dake tafe.
|
70
|
<|title|>Bukarti ga Turji: In ka cika jarumi ka fito kayi gaba-da-gaba da sojoji
<|section|>news
Fitaccen mai sharhi kan lamuran tsaro a Najeriya, Barista Audu Bulama Bukarti ya bayyana jagoran ƴan fashin jeji da su ka addabi Arewa maso yamma, Bello Turji a matsayin matsoraci wanda ba zai iya yin gaba da gaba da sojoji ba. Bulama na mayar da martani ne bayan kalaman Bello Turji wanda yayi a wani faifan bidiyo a kwanan nan, inda ya ke caccakar Bukarti din. A sakon da ya wallafa a shafin sa na X, Bukarti ya ce Turji na kokarin kawar da kansa daga matsayin ɗan ta’adda zuwa mai ikirarin kare Fulani, inda ya ce, hakan ba zai yi tasiri ba domin duniya tasan ko waye shi. “Al’ummar Fulani sun barranta dashi saboda suna ganin sa a matsayin mai lefi dake ɓata musu suna. “Sannan kalaman na Turji yayi su ne don ɓata irin mu dake tona ayyukan sa na ta’addanci da kuma yin kira ga Gwamnati ta ɗau mataki n soji a kan sa da yaransa. “Shi ba komai bane, illa matsoraci da yake zaluntar waɗanda basu ji ba basu gani ba kuma ya dinga musu sata kamar ɓera. Idan shi yana jin jarumi ne to ya fito yayi gaba da gaba da sojoji”, inji Bulama.
|
71
|
<|title|>Dillalan mai sun kaiwa Tinubu ƙorafin cewa man dizel din mu ya yi arha — Dangote
<|section|>news
Dillalan man fetur a Nijeriya sun rubuta wasikar koke ga shugaban ƙasa Bola Tinubu cewa karya farashin dizel zuwa Naira 900 duk lita da matatar mai ta Dangote ta yi na yin illa ga kasuwancinsu. Devakumar Edwin, mataimakin shugaban rukunin kamfanonin Dangote ne ya bayyana hakan yayin wata tattaunawa ta shafin X wacce Nairametrics ta shirya. “Dillalan man fetur a Nijeriya sun rubuta wasika ga shugaban ƙasa Tinubu domin yin korafi kan cewa farashin man dizel a matatar mu ya yi kasa daga 1200 zuwa 1000 a yayin da yanzu ya kara karye wa zuwa 900 duk lita wanda hakan yake shafar kasuwanci su”,inji shi. Edwin ya bayyana wasu daga cikin kalubale da matatar man ta Dangote ke fuskanta da kuma tasirinta ga man da ƙasar nan ke samarwa da kuma farashi. Acewarsa, matatar wacce ke unguwar Lekki a jihar Legas, na ta fafutukar siyar da tanka 29 na Dizel a duk rana sakamakon ƙarancin siyan man daga ƴan kasuwar gida. “Sakamakon wannan ƙarancin siyan man daga ƴan kasuwar gida, matatar ta fitar da mafi yawancin man dizel da na jirgin sama zuwa ƙasashen waje”, inji shi. Tun da farko, Edwin ya ce matatar man zata dinga fitar da shi waje idan kamfanin NNPCL ya ƙi siya. “Muna fitar da man jiragen sama, muna samar da Kalanzir”. Edwin ya kuma bayyana mamakin sa kan yadda matatar ta fara samun kalubale a yayin da ta shirya fara aiki.
|
72
|
<|title|>Ambaliya: Mutane 30 ne su ka rasu a Maiduguri — NEMA
<|section|>news
Ambaliyar ruwa da ta afkawa birnin Maiduguri na jihar Borno ta jawo asarar rayuka 30, inji hukumomi a jiya Laraba. Daruruwan gidaje ne ambaliyar ta tafi dasu, wacce kuma ta yi barna a gonaki da unguwanni da wuraren kasuwanci. Ambaliyar ta faru ne bayan ballewar Dam din Alau dake garin Maiduguri. “Adadin mutanen da suka mutu sun kai 30”, inji mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA, Ezekiel Manzo. Kodayake, mazauna garin sun ce adadin wadanda suka rasu ka iya fin haka saboda har yanzu akwai mutane ciki har da kananan yara da ba a gansu ba. “Babu wani da yasan adadin mutanen da suka mutu sakamakon wannan iftila’i”, inji Tasiu Abdullahi, mazaunin yankin Gwange da lamarin ya shafa. ” Zasu iya kai 60 ko fiye da haka”, inji wani direban Taxi, Babagana Modu. Wuraren da ambaliyar tafi shafa sun hada da: Kasuwar Monday Market da fadar Shehun Borno da Shehuri da Gwange da Adamkolo da Gamboru da Fori da Bulabulin da Moromoro da gadar Kwastom. Ambaliyar ta tafiyar da makabartar Gwange inda ake ganin gawarwaki na yawo cikin ruwa a kan hanya. Marasa lafiya a asibitin koyarwa na Maiduguri ma abin ya shafe su. Gwamna, Babagana Zulum na jihar Borno ya ce ambaliyar ta shafi a kalla mutane Miliyan 1.
|
73
|
<|title|>Fasto ya kashe matarsa da wuka a Anambra
<|section|>news
Wani Fasto mai suna Elijah Okafor ya daɓa wa matarsa Ogechukwu wuka har lahira a jihar Anambra. Daily Trust ta rawaito cewa Okafor ya kashe matar ta sa a kauyen Nimo, karamar hukumar Njikoka ta jihar, a ranar 13 ga Agusta, 2024. Iyalan mamacin sun kai rahoton faruwar lamarin ga ma’aikatar harkokin mata da walwalar jama’a ta jihar. Bayan samun labarin, kwamishiniyar harkokin mata da walwalar jama’a, Ify Obinabo, ta bayar da umarnin gudanar da bincike kan lamarin. A cikin wata sanarwa da ma’aikatar ta fitar ta ba da cikakken bayani kan lamarin da kuma matakan da ake dauka na tabbatar da adalci. Obinabo ya sha alwashin cewa gwamnatin jihar za ta binciki lamarin tare da yin kira ga kowa da kowa da ya ba da hadin kai kan lamarin.
|
74
|
<|title|>Kaduna: An kama ɗan shekara 74 da ya shafe shekaru 10 ya na sata a masallatai
<|section|>news
Dubun wani tsoho ɗan shekara 74 ta cika, inda aka kama shi yana satar tabarmin masallatai a Jihar Kaduna. Aminiya ta rawaito cewa tsohon dai ya amsa cewa ya shafe sama da shekaru 10 yana shiga masallatai ya sace tabarminsu. Ya kara da cewa wani lokaci ma yakan saci agogon bangon masallatai, amma bai taɓa satar Alkur’ani ba. An kama wannan tsoho yana satar tabarmin ne a wani ƙaramin masallaci da ke unguwar Rigasa a Karamar Hukumar Igabi. Dubunsa ta cika ne a masallacin da ke layin Sarkin Bori Sule, a ranar Talata, bayan an addabi masallatan unguwar da satar sabbin tabarmi. Mutumin ya kuma amsa cewa karo na biyu ke nan da ya saci tabarmi daga masallacin da aka kama shi. Ya ce, “Da ni ake sallar jam’i, idan mutane suka fice sai in dauke sabbin tabarmi. Nakan sayar da kowacce a kan N1,500 zuwa N2,000.”
|
75
|
<|title|>Wani asibiti ya ƙaddamar da na’urar maganin cutar shawara da ƙwaƙwalwa ga jarirai a Kano
<|section|>news
Wani asibiti mai zaman kan sa, Best Choice ya ɗauki gabaren kula da kiwon lafiyar jarirai tare da ƙaddamar da Sashin fasaha don kula da Lafiyar Jarirai da aka tsara don magance ciwon shawara da hana lalacewar kwakwalwar ga jarirai. A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugaban Asibitin, Auwal Muhammad Lawal, ya lura cewa na urar ita ce irin ta ta farko wanda kwararrun likitoci ke amfani da ita wajan juyen jini cikin fasaha don inganta sakamakon jiyya ga yara. A nan bangaren Dr Abdulmalik Saminu ya bayyana cewa na’ura ce mai cike da fasaha dake ɗaukar nauyin fitowar haske kaso 70% na ban mamaki dake daidaita buƙatar ƙari ko juyen jini. Ya kara da cewa bullo da wannan na’ura ta zamani ya nuna wani gagarumin ci gaba ne da Asibitin Best Choice ya bullo da shi don kula da kiwon lafiyar jarirai. Saminu yace sashin Kula da Lafiyar Jarirai na iya yin maganin ciwon shawara yadda ya kamata cikin kwarewa ba tare da daukan yin doguwar jinya ga iyalai ba da kuma saukin kashe kudade. “Mun fahimci irin yadda iyaye ke faman shan wahala game da yanayin lafiyar kananan yara” “Saboda haka ne muka mai da hankali kan wannan fasaha don sauƙaƙe nauyin da ke kan iyalai da kuma samar wa yara yanayi mafi kyawu, domin samun rayuwa mai kyau”. In Ji Auwal. Shugaban Asibitin ya bayyana cewa na’urar ita ce irin ta ta farko a Arewacin Najeriya, kuma ta uku a fadin Najeriya, kuma tana ba da cikakkiyar kariya da maganin jiyya ga jarirai. Dr. Abdulmalik Saminu, babban kwararre likita ne a fannin kiwon lafiya ya bayyana fatansa cewa wannan ci gaban zai kara karfafa matsayin asibitin Best Choice a matsayin jagora a fannin kula da kiwon lafiyar kananan yara, tare da baiwa iyalai kwarin gwiwa kan kula da ‘yan uwansu. Saminu daga nan ya godewa mamallakin asibitin bisa namijin kokarin da yayi na samar da wannan wannan fasaha ta zamani duk da bala’in tsadarta. Da wannan sashin Kula da Lafiyar Jarirai ne, iyalai da yan uwa ba sa buƙatar neman tafiya ƙasashen waje don neman magani, kamar yadda asibitin Best Choice ke ba da kulawa ta musamman a cikin gida.
|
76
|
<|title|>Ambaliya: Al’umma sun fara komawa mahallansu yayin da ruwa ya fara janye wa a Maiduguri
<|section|>news
Mazauna garin Maiduguri da ruwa ya raba da muhallansu daga madatsar ruwa ta Alau sun fara komawa gidajensu yayin da ruwan ke raguwa a hankali. Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya ruwaito cewa da yawa daga cikin wadanda ambaliyar ta shafa da suka kwana a waje sun ce duk da cewa ruwan ya lafa, suna son tantance asarar da suka yi ne a gidajen na su. “Muna gaggawar ganin abin da ya rage na gidajenmu da kuma kwashe sauran abubuwan da su ka rage daga dukiyoyinmu da har yanzu za mu iya amfani da su,” in ji Ali Bana da ake unguwar Gwange. Shi ma Musa Abdullahi na unguwar Gomari, ya ce ya samu damar zuwa gidansa. “Har yanzu gidana ya na cike da ruwa. Duba da yanayin, gaskiya sai mun kara kwanaki a waje kafin mu koma gidajen mu” in ji Abdullahi. Hukumomi sun ce fiye da mutane 239,000 ne ambaliyar ta shafa. “Ambaliyar ta tilasta wa wasu mutanen da abin ya shafa kaura kai tsaye zuwa sansanin yan gudun hijira na Muna, wanda tuni akwai ‘yan gudun hijira sama da 50,000 a cikin sa.
|
77
|
<|title|>Zaɓen ƙananan hukumomi a Kano: Gwaji ya nuna ƴan takara 20 na shaye-shaye – NDLEA
<|section|>news
A kalla ƴan takara 20 a zaben kananan hukumomi dake tafe a jihar Kano a ka samu suna shaye-shaye a gwajin da hukumar NDLEA ta yi musu. Kwamandan hukumar ta NDLEA na Kano, Abubakar Idris Ahmad ne ya tabbatar da hakan ga jaridar Daily Trust a ofishin sa. Ya ce, wasu daga cikin ƴan takarar, gwaji ya nuna suna shan codeine da ganyen wiwi. “Masu neman takara 20 da jam’iyyar NNPP ta gabatar mana, gwaji ya nuna suna shan muggan kwayoyi kuma ana ci gaba da gwajin.” Sai dai ya ce babu mace a masu neman takarar da gwaji ya nuna tana shan kwaya. Ya ce, iya jam’iyyar NNPP ce ta gabatar da masu neman takarar don gwajin shan kwaya a yayin da ake shirin mika sunayen ‘yan takara ga hukumar Zabe ta KANSIE. Hukumar zaben dai ta sanya ranar 26 ga watan Oktoba don gudanar da zaben kananan hukumomi a jihar
|
78
|
<|title|>Ambaliya: Sama da mutane 200,000 sun rasa mahallai inda yara da dama su ka ɓace a Maiduguri
<|section|>news
Ambaliyar ruwa da ta afku a Maiduguri, babban birnin jihar Borno da sanyin safiyar jiya, ta mamaye daruruwan gidaje tare da lalata dimbin dukiya. Hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta tabbatar da cewa sama da mutane 200,000 ne suka rasa muhallansu. NEMA ta ce mutane da ƙananan yara da ba a san adadin su ba sun ɓace, inda ta tabbatar da cewa ambaliyar ta lalata kadarori da dama da suka hada da, gidaje, gonaki da wuraren kasuwanci. Mazauna garin, wadanda akasarin su ‘yan karamar hukumar Jere ne, an tilasta musu barin gidajensu. Ambaliyar ruwan ta biyo bayan rugujewar madatsar ruwa ta Alau, wadda daga kimanin kilomita 10 zuwa cikin babban birnin jihar. Matsuguni da wuraren kasuwanci sun nutse cikin ruwa da suka hada da shahararriyar Kasuwar Monday da dubban gidaje da kadarori, kamar fadar Shehun Borno, Shehuri, Gwange, Adamkolo, Gamboru, Fori, Bulabulin, unguwannin gidan waya, Moromoro, da kwastam. Gadar da dai sauran su ma abin ya shafa. Yawancin mazauna garin da suka zanta da Daily Trust sun ce ba su iya gano ‘yan uwansu ba a halin yanzu.
|
79
|
<|title|>Gwamnatin Borno za ta maida waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa zuwa mahallansu cikin makonni biyu — Shettima
<|section|>news
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya ce gwamnatin jihar Borno za ta yi kokari ta maida al’ummar da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maiduguri zuwa mahallansu cikin mako ɗaya zuwa biyu. Shettima ya baiyana hakan ne a yayin da ya ke yi wa al’ummar jawabi a Sansanin yan gudun hijira na Bakasi, yayin ziyarar gani-da-ido da ya kai a Maiduguri a jiya Talata. Ya ce za a yi gaggawar maida al’ummar da ambaliyar ta shafa zuwa mahallansu saboda “ba ma son a sake samun wasu sabbin sansanonin ƴan gudun hijira. Ba abin so ko alfahari ba ne a rika samun sabbin ‘IDP Camps’.” Bayan ya zagaya guraren da abin ya shafa, Shettima ya tabbatar da cewa gwamnatin taraiya da ta jiha da hukumomin agaji kamar su NEMA, SEMA, NEDC, da RC zasu hada kai wajen tallafawa waɗanda ambaliyar ta shafa cikin gaggawa. “Ba maganar siyasa, da gaske mu ke za mu tallafa muku cikin gaggawa a kan wannan mawuyacin hali da ku ka tsinci kan ku. “In Sha Allah gwamnatin jiha, cikin sati daya ko biyu za ta maida kowa mahallinsa. “Za mu hada kai da hukumomin agaji da gwamnatin jihar Borno wajen kawo muku dauki. “Mu na yi muku jaje da kuma tausaya wa bisa wannan ibtila’in da Allah Ya aiko mana da shi,” in ji Shettima.
|
80
|
<|title|>Tinubu ya bada umarnin gaggauta kwashe mutanen da ambaliyar ruwa ta ɗaiɗaita a Maidugur
<|section|>news
Shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna damuwa kan ambaliyar ruwa da ta shafi birnin Maiduguri na jihar Borno. Ambaliyar ruwan wacce ba a samu irin ta tsawon shekaru ba a jihar ta raba dubban mutane da muhallansu, inda kuma ta shafi wurare da dama ciki har da asibitin koyarwa na Maiduguri. A wata sanarwa da mai baiwa shugaban kasa shawara na mussaman kan yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, Tinubu ya yi jaje ga gwamnati da al’ummar jihar ta Borno. “Yayin da hukumomi ke tantance barnar da ambaliyar ta haifar, shugaban kasa ya yi kira da a gaggauta dauke mutane daga wuraren da abin ya shafa. ” Shugaban kasa Tinubu ya tabbatarwa da Gwamna Babagana Zulum cewa Gwamnatin tarayya a shirye take wajen hada kai da jihar don samar da agajin gaggawa ga al’ummar da abin ya shafa”, inji sanarwar. Haka kuma, shugaban kasar ya umarci hukumar bada agajin gaggawa ta NEMA ta kai kayan tallafi ga wadanda ambaliyar ruwan ta sha fa.
|
81
|
<|title|>Babu shugabanci a LP, in ji Sanata a jam’iyyar
<|section|>news
Victor Umeh, Sanata mai wakiltar Anambra to Tsakiya baiyana cewa a halin yanzu dai jam’iyyar Labour (LP) ba ta da shugabanci a Nijeriya. Ya baiyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Siyasa a Yau a gidan talabijin na Channels. Umeh, wanda kusa ne a LP, ya fadi hakan ne a yayin da aka yi masa tambaya akan rikicin da ke jam’iyyar ta labour. Hakan na zuwa ne yayin da dan takarar shugabancin ƙasa a LP a zaɓen 2023, Peter Obi ke kokarin kawo sauyin a shugabancin jam’iyyar a fadin ƙasa.
|
82
|
<|title|>Rundunar sojin-ƙasa ta yarda cewa sojoji na ta ajiye aiki, amma ta baiyana dalili
<|section|>news
Rundunar Sojin-ƙasan Najeriya ta ce yin ritaya na ƙashin kai da sallamar ma’aikata abu ne na yau da kullun kuma ya yi daidai da ka’idojin da aka gindaya kamar yadda ya ke kunshe a cikin Ka’idoji da Sharuɗɗan Aikin soja, wanda ya shafi manya da kananan sojoji. Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Maj.-Gen. Onyema Nwachukwu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a jiya Lahadi a Abuja. Nwachukwu ya caccaki labarin da wasu kafafen yada labarai suka buga kwanan nan, inda su ka rawaito yadda sojoji ke barin aiki saboda cin hanci da rashawa, rashin walwala da makamantansu. Ya ce rahotannin ba wai yaudara ce kawai ba, har ma da yunkurin shuka ɓatanci da kiyayya tare da bata sunan kishin ƙasa na ma’aikata da mutuncin sojojin Nijeriya. A cewarsa, yana da matukar muhimmanci a fayyace cewa aikin sojan Najeriya, kamar yawancin sojoji a duniya, na ganin dama ne ba. “Saboda haka, wannan ya na nufin cewa soja na da damar barin aiki a duk sanda ya ga dama kuma mu ma haka ya ke a rundunar sojin-ƙasa. “Ma’aikata suna da ‘yancin ajiye aiki daga lokaci zuwa lokaci bisa ga ka’idojin da aka gindaya “barin aiki a rundunar sojojin Najeriya abu ne na yau da kullun kuma da ya yi daidai da tsarin da aka gindaya,” in ji shi.
|
83
|
<|title|>Watanni 30 kenan ba a biya mu alawus ba, jami’an tsaron bodojin Nijeriya sun koka
<|section|>news
Wasu jami’an Hukumar Kwastam ta Ƙasa (NCS) da na Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (NIS) da aka tura kan iyakokin Najeriya sun koka da rashin biyansu alawus-alawus din su na tsawon shekaru biyu da rabi, lamarin da ya bar su cikin wani mawuyaci. Ma’aikatan sun yi ikirarin cewa sun shafe sama da shekaru biyar su na aikin tsaro a kan iyakokin, tun daga gwamnatin da ta gabata; al’amarin da suka ce ba a saba gani ba ne kuma ga kashe musu karsashin aikin. Daily Trust ta rawaito cewa daya daga cikin jami’an tsaron da aka tura kan iyakokin ya shaida wa sashen Hausa na BBC a jiya Lahadi cewa: “Muna cikin wani mawuyacin hali. Tun gwamnatin Shugaba Buhari aka tura mu kan iyakokin kasa, amma duk da haka, ba mu samu alawus din mu ba tsawon shekara biyu da rabi.” Ma’aikatan, wadanda suka nemi a sakaya sunansu, sun bayyana yanayin rayuwarsu a matsayin abin bakin ciki, tare da yin kira ga hukumomi da su magance halin da suke ciki. Ya ci gaba da cewa, “Da farko an tura mu ne tare da sojoji da ‘yan sanda da kuma jami’an DSS. Ana biyan mu dukkan alawus-alawus akan lokaci kafin daga bisani abubuwa su taɓarɓare. “Ba a biya mu alawus ba na tsawon wata 30. Hakan ya fara ne a kwanaki na karshe na Shugaba Buhari. Da ya ke mayar da martani a lokacin da ya ke zantawa da Daily Trust, Kakakin Hukumar Kwastam, Abdullahi Maiwada ya ce hukumar ta san halin da ake ciki kuma tana yin wasu gyare-gyare ne akan lamarin. Shi kuma kakakin hukumar NIS, Kenneth Udo, bayan an tuntube shi, ya yi alkawarin yin bincike tare da tuntubar Daily Trust nan gaba.
|
84
|
<|title|>APC ga Kawu Sumaila: Muna addu’ar Allah Ya dawo da kai cikin mu
<|section|>news
Jam’iyyar adawa ta APC a jihar Kano ta nuna fatan Sanata mai wakiltar Kano ta Kudu, Sanata Abdulrahman Kawu Sumaila ya dawo gidan sa na siyasa da ya bari. Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Sanata Sumaila ya fice daga APC ne a gabanin zaɓen 2023, inda ya sauya sheka zuwa jam’iyyar adawa (a wancan lokacin) ta NNPP kuma ya tsaya takara a nan har ya ci zaɓe. Sai dai kuma a yayin kaddamar da rabon kayan abinci da shugaban kasa ya bayar a rabawa talakawa a Kano a yau Lahadi, kakakin jam’iyyar APC a Kano, Ahmed Aruwa, ya yi fatan Kawu Sumaila ya dawo jam’iyyar ta su. Yayin da ya ke yi mika sannu da zuwa ga manyan baki da su ka halarci taron, Aruwa, cikin barkwanci ya ce “Sanata Kawu Sumaila, Sanatan alheri. Allah Ya maida koko masaki. Allah Ya dawo mana da kai jam’iyyar APC,” Wakilin Daily Nigerian Hausa ya rawaito cewa bayan da Aruwa ya fadi wannan kalamai, sai gurin ya rude da shewa da cewa “ameen”. Sai dai kuma Daily Nigerian Hausa ta gano cewa Aruwa ya baiyana wannan fata ne a kashin kan sa ba da yawun jam’iyyar APC ba.
|
85
|
<|title|>Sarkin Potiskum ya nuna goyon baya ga sarautar Sarkin Kano Sanusi
<|section|>news
Mai Martaba Sarkin Potiskum Alh. Umar Bubaram Ibn Wuriwa Bauya ya yi mubaya’a ga Sarkin Kano, Khalifa Dr. Muhammad Sanusi II. Sarki Bauya ya nuna goyon bayan ne yayin da ya ziyarci Sarki Sanusi a fadar sa da ke Kano. Wata majiya a masarautar Kano ta shaida cewa Bauya shi ne Sarki na farko da ya ziyarci Fadar Sarki Sanusi tun bayan dawowarsa a karo na biyu. “in da ya nuna goyon bayan Masarautarsa da fatan Alkhairi ga Sarki. “Mai Martaba Sarki Muhammad Sanusi ya ce wannan shine nuna soyayya da kauna wacce bazai taba mantawa da ita ba,” in ji majiyar.
|
86
|
<|title|>Ƴan Nijeriya na cikin yunwa, ka ɗauki matakan gaggawa — Jigo a APC ya faɗawa Tinubu
<|section|>news
Olatunbosun Oyintiloye, wani jigo a jam’iyyar APC a jihar Osun, ya roki shugaban kasa Tinubu ya yi saurin daukar mataki kan karuwar yunwa da matsin tattalin arziki da ake fuskanta a kasar nan. Mista Oyintiloye, wanda tsohon dan majalisa ne yayi rokon yayin ganawa da manema labarai a birnin Osogbo a ranar Lahadi. Ya ce wahalar rayuwa da yunwa da ‘yan Najeriya ke fuskanta a yanzu na bukatar a dau matakan gaggawa. Ya ce duk da cewa babu makawa, shugaban kasa Tinubu na aiki tukuru don kawo karshen wahalar da ake fuskanta, amma akwai bukatar kari. Mista Oyintiloye, wanda mamba ne a kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na APC, ya ce matsin tattalin arziki da ake fuskanta shi ya haifar da hauhawar farashin kayan abinci da na mai da wutar lantarki. Daga karshe ya roki ‘yan Nijeriya da su ci gaba da bada goyan baya ga gwamnatin shugaban kasa Tinubu.
|
87
|
<|title|>Ni ba juya bace, mai-ɗakin gwamnan Edo ta yi martani ga Adams Oshiomhole
<|section|>news
Matar Gwamnan jihar Edo, Besty Obaseki ta shawarci matan da basa haihuwa kan kada gwiwarsu tayi sanyi domin zasu iya cika muradunsu ta mabanbanta hanyoyi ba iya zama uwaye ba. Daily Trust ta rawaito cewa matar Gwamnan na bayani ne a ranar Asabar a wani taron tattaunawa ta kafar Internet wanda matan Edo dake zaune a kasashen ketare suka shirya ga dan takarar jam’iyyar PDP na gwamnan jihar, Asue Ighodalo. “Ni ba juya bace; ina cikin nishadi kuma ina cimma burina”, inji ta. Tana mayar da martani ne kan tambayar da wata mata tayi mata game da kalaman tsohon Gwamna, Sanata Adams Oshiomhole kan cewa bata haihuwa. Oshiomhole, yayi bayanin ne don mayar da martani kan kalaman Besty wacce ta ce, Ighodalo ne kadai yake da mata a wadanda suke neman kujerar Gwamnan jihar. Ta ce ta taba samun barin ciki wanda dan yazo a mace.
|
88
|
<|title|>Dangote zai iya sayar da man sa ga kowa ba mu kadai ba — NNPCL
<|section|>news
Babban Kamfanin mai na Ƙasa, NNPCL ya musanta zargin da ya ce ƙungiyar kare haƙƙin Musulmi ta Najeriya, MURIC ta yi masa na yi wa matatar mai ta Dangote maƙarƙashiya. MURIC ta yi zargin cewa ƙarin kuɗin mai da NNPCL ya sanar a baya-bayan nan zai hana matatar Dangoten sayar da man a farashi mai rahusa, sannan ta yi zargin cewa kamfanin NNPCL ne kawai zai riƙa sayen mai daga matatar. To sai dai cikin wata sanarwa da kamfanin ya fitar ranar Asabar, ya musanta zargin, yana mai cewa kasuwa ce ke ƙayyade farashin man kowace matata ciki kuwa har da ta Dangote. ”Ƙarin kuɗin mai da aka samu a baya-bayan nan ba zai hana matatar Dangote ko duk wata matata a cikin ƙasar nan samun ciniki ba. Idan ma suna ganin kamar kuɗin ya yi yawa, to matatar ta samu damar da za ta rage farashi domin samun ciniki a kasuwa”, in ji sanarwar. Haka kuma NNPCL ɗin ya ce babu tabbacin samun ragin rafashi kan man da aka tace a gida fiye da yadda ake sayar da shi a kasuwar duniya, kamar yadda matatar Dangoten ta tabbatar masa. Kamfanin NNPCL, ya ƙara da cewa zai sayi man Dangote ne kawai idan farashin man a kasuwar duniya ya fi yadda ake sayar da shi a Najeriya, don haka matatar Dangote da sauran matatun cikin gida na da damar sayar da man ga duk wanda ke buƙata a kan farashin da suka daidaita. ”NNPCL ba shi da niyyar kankane sayar da man shi kaɗai a fagen kasuwancin da kowa ke da damar shiga a dama da shi, don haka maganar a ce NNPCL ne zai sayi mai daga matatar ba ta taso ba,” in ji sanarwa. Kamfanin ya kuma ce babu ta yadda zai yi maƙarƙashiya ga kasuwancin da ya zuba hannun jarin biliyoyin daloli a cikinsa. BBC Hausa
|
89
|
<|title|>YANZU-YANZU: Ngelale ya ajiye aikinsa a matsayin mai magana da yawun shugaban ƙasa Tinubu
<|section|>news
Mai magana da yawun shugaban kasa Bola Tinubu, Chief Ajuri Ngelale ya ajiye aiki sakamakon rashin lafiya. Ajuri, ya bayyana hakan ne a wata takaitacciyar sanarwa da ya fitar a yau Asabar. “A ranar Juma’a, na mika takarda ga shugaban ma’aikata na fadar shugaban kasa, inda na ke shaida masa cewa na tafi hutu na sai-baba-ta-gani domin mayar da hankali kan batun rashin lafiya wanda hakan abun damuwa ne ga ahali na. ” A yayin da na ke godiya kan wannan nauyi da aka dora min wanda yanzu ya kai matakin yanke shawarar dakatawa da aikina a matsayin mai baiwa shugaban kasa shawara a fannin yada labarai kuma mai magana da yawunsa; jakada na musaaman ga shugaban kasa a fannin sauyin yanayi kuma shugaban kwamitin shugaban kasa kan shirin Evergreen. “Na dau wannan matakin ne bayan tuntubar iyalina a yayin da rashin lafiya ya tsananta a gida na. Zan dawo bakin aiki da zarar waraka ta samu kuma lokaci ya bada dama,” in ji Ngelale.
|
90
|
<|title|>NADDC za ta yi taron wayar da kai don haskawa matasa damammaki a harkar ƙera ababen-hawa da sufuri
<|section|>news
Hukumar Kula da Ƙere-ƙere da Samar da Ababen-hawa ta Ƙasa, NADDC, da hadin gwiwa da Ofishin Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Cigaban Matasa, Sanya Ido da Aiwatar da ayyuka, na daf da yin wani gangamin taro na bajekolin fasaha da nufin haskawa matasa damammaki a ɓangaren ababen-hawa da sufuri a Nijeriya. Taron, wanda za a gudanar a ranar 11 da 12 ga watan Satumba a Musa Yar’Adua Centre in Abuja, zai haska damammaki a ɓangaren sabuwar fasahar amfani da iskar gas a ababen-hawa, CNG, amfaninda wajen bunkasa tattalin arziki da kuma amfanin sa da tsari da yake da shi a ababen-hawa. Mr. Rosilu Emmanuel, Mataimaki na Musamman kan dabarun aiki ga shugaban, NADDC, Mr. Oluwemimo Joseph, a wata sanarwa da ya fitar ya ce taron zai nunawa matasa hanyoyin samun arziki a bangaren ababen-hawa da sufuri. Ya kara da cewa a taron, NADDC za ta ƙaddamar da gasar zanen ƙera mota mai amfani da iskar gas domin baiwa matasa damar bajekolin fasahar su da kuma karfafa musu gwiwa a fannin. Ya kara da cewa “masu sha’awar shiga gasar za su aiko da faifain bidiyo na mintinan 2 zuwa 3 su nuna irin fasahar su a ciki zuwa addressing imel na [email protected] daga ranar 1 zuwa 9 ga watan Satumba.” Ya kara da cewa masana da masu ruwa da tsaki a harkar ƙere-ƙeren ababen-hawa da sufuri ne za su halarci taron. Ya kara da cewa; Manyan baki da za su halarci taron sun hada da Bola Ahmed Tinubu, GCFR, Hon. (Dr.) Doris Uzoka-Anite, Ministan Kasuwanci da Masana’antu, Shugaban hukumar NADDC, Mr. Oluwemimo Joseph Osanipin, Mataimakin Shugaban ƙasa kan harkokin matasa, Hon. Titilope Gbadamosi, inda hakan zai kara wa matasa kaimi wajen cika burin su a fannin,” in ji sanarwar.
|
91
|
<|title|>Yadda ƴan bindiga suka ciyar da karnukan su da naman gawar dan uwa na a Sakkwato — Malami
<|section|>news
Fitaccen Malamin addinin Musulunci a jihar Sokoto, Sheikh Bashar Danfili, ya roki jama’a su taimaka musu da tallafin kudi bayan ƴan bindiga sun yi garkuwa da ƴan uwansa. Daily Trust ta rawaito cewa a wani gajeren faifen bidiyo da ya yadu a shafukan sada zumunta, Malamin ya ce mutanen da aka sace sun hada da wani mutum da mahaifiyarsa da kishiyarta da matasansa biyu da kuma ƙanwar sa. Ya ce, ƴan bindigar sun nemi kudade masu yawa, wanda a yanzu sun kasa hadawa, inda ya kara da cewa, wa’adin da ƴan bindigar suka basu na kara kusanto wa. Malamin ya ce: “Yan bindiga sun sace makusanta na. Ba sai na fadi sunansu ba. “Suna kan hanyar su ta zuwa wani kauye a yayin da aka kwashe su. “Sun kashe direban motar kuma suka baiwa karnunaka naman sa suka cinye. ” Sai dai ragowar mutanen har yanzu suna hannunsu, ciki har da miji da matan nasa da mahaifiyarsa. “Yan bindigar sun bukaci miliyoyin kudade, wanda mun kasa hadawa. ” Ni Malami ne, bani da komai. Aiki na shi ne koyar da al’umma da littafan da kuke gani a baya na. “Kuma sun bamu wa’adin lokacin da za a kai kudin, idan ba a kai ba zasu kashe su gabadaya. ” Nasan zasu iya yin hakan, duba da abinda ya faru da Sarki a kwanan nan. “A don haka nake neman taimako daga al’umma domin biyan kudin fansa don sako su”.
|
92
|
<|title|>Tawogar wasan Polo ta kai wa Sarki Sanusi ziyarar neman tabarraki
<|section|>news
Tawogar wasan ƙwallon-doki ta Polo, ƙarƙashin jagorancin Tajuddeen Aminu Dantata ta kai wa Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi ko ziyarar neman tabarraki. Da ya ke jawabi a yayin ziyarar, Bashir Dantata, dan uwa ga Tajuddeen, ya ce sun zo fada ne domin shaida wa Sarki shirye-shiryen su na fara gasar ƙwallon-doki kwanan nan a Kano. A cewar sa, sun kawo wa Sarki ziyara ne domin neman tabarraki da kuma gaiyatar sa a ranar da za a bude gasar da kuma ranar rufewa. Ya ce muhimmancin Sarki a matsayin uban ƙasa shi ya sanya su ka kawo masa ziyara kuma su ke neman albarkar sa. A nashi jawabin, Sarki Sanusi ko, ya yaba musu bisa ganin dacewar shaida masa gasar tare da yi musu fatan alheri. Ya shaida musu cewa masarautar na same da shirye-shirye da su ke yi ma gasar, inda ya yi musu fatan yin nasara da kuma gama wa lafiya. “Kuma ina horon ku da ku ci gaba da rike abubuwan da magabatan ku su ka bar muku, ku kuma rika karfafa wa na kasa da ku don samun ci gaba mai dorewa,” in ji shi.
|
93
|
<|title|>Tinubu ya gana da shugaban kasar China, Xi Jinping
<|section|>news
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya yi wata ganawa da shugaban ƙasar China Xi Jinping a yau Talata. Ganawar ta wakana ne a Beijing, babban birnin ƙasar ta China. A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun shugaba Tinubu, Ajuri Naglale ya ce shugabannin biyu sun amince da yauƙaƙa dangantakar da ke tsakanin ƙasashen biyu zuwa matakin amintaka. A cikin bayaninsa, shugaba Tinubu ya ce “Wannan ziyara ce mai matuƙar muhimmanci ga Najeriya da kuma Afirka baki ɗaya, kasancewar na zo nan ne a matsayi na na shugaban ƙungiyar haɓɓaka tattalin arziƙin ƙasashen Afirka (Ecowas).” “Dangantakar da ke tsakanin Najeriya da China ta daɗe, kimanin rabin ƙarni, saboda haka akwai buƙatar a ƙara ƙarfafa wannan dangantaka domin bunƙasa harkar kasuwanci da ci gaban tattalin arziƙi,” in ji Tinubu. Ya ƙara da cewa akwai damarmaki sosai a Najeriya kasancewar ta ƙasa mafi yawan al’umma a nahiyar Afirka, wadda kuma ke da ɗinbin matasa da za su taimaka wajen ciyar da tattalin arziƙi gaba. Tinubu na ziyara ne a China a domin halartar taron bunƙasa hulɗa tsakanin ƙasashen Afirka da China.
|
94
|
<|title|>Nijeriya ce ta biyu a ƙarancin abinci a duniya — Bill Gates
<|section|>news
Shugaban gidauniyar haɗaka ta Bill & Melinda Gates, Bill Gates, ya ce Najeriya ce kasa ta biyu a jerin kasashe masu fama da karancin abinci a duniya. Ya bayyana hakan ne a lokacin da ya ke zantawa da wata kwararriya a fannin yada labarai, Lara Adekoro, kan yanayin abinci mai gina jiki a Najeriya da kuma nahiyar Afirka. Ya ce lamarin ya kara tabarbare wa je sakamakon sauyin yanayi da dai sauran matsaloli. A cewarsa, filayen noma sun shafe sakamakon sauyin yanayi wanda ya haifar da tashin gwauron farashin abinci. Ya ce gidauniyarsa tana aiki tare da Cibiyar Kiwon Lafiya da sauran masu ruwa da tsaki don kara fahimtar matsalar yunwa da yanayi ke haifarwa.
|
95
|
<|title|>Ba ƙwace motocin sojoji ƴan bindiga su ka yi ba – Mazauna Zamfara
<|section|>news
Wasu mazauna garin Zurmi da ke karamar hukumar Zurmi a jihar Zamfara sun karyata rade-radin da ake ta yadawa na kwace wasu motoci biyu dauke da makamai daga hannun sojoji da wani dan bindiga mai suna Bello Turji ya yi. Da ya ke zantawa da Daily Trust, wani mazaunin garin Zurmi ya ce ‘yan bindigar ba su taba kwace motocin daga hannun sojoji ba, sai dai sun same su makale a cikin daji suka banka musu wuta. Ya bayyana cewa, wannan abin takaicin ya faru ne a ranar Juma’ar da ta gabata a kauyen Kwasabawa yayin da sojoji ke shiga daji domin gudanar da aiki, kwatsam sai ga motar su ta makale rabin hanya cikin daji. “Bayanan da muka samu sun nuna cewa sojoji sun samu labarin cewa ‘yan bindigar na yin taro a wani wuri a cikin dajin, don haka suka yanke shawarar isa wurin da nufin yakar su amma basu kai ga karasawa ba motar ta tsaya. Da farko sojoji da jami’an hukumar kare hakkin al’umma ta Zamfara (CPG) sun yi wa motocin sojojin gadin don hana ‘yan bindigan shiga su, amma daga baya suka yi watsi da su suka bar wurin.” Wani mazaunin yankin, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce da a ce sojoji sun samu karfin gwiwa a kan lokaci da lamarin ba zai faru ba; yana mai cewa ‘yan bindigar ba za su shiga motocin ba. Ya ce: “A gaskiya ‘yan bindigar ba su yi wa sojoji harbin bindiga ba, sun kuma kwace motocin sojojin amma sai da sojoji suka bar wajen. “A gaskiya sojoji sun zauna a kusa da motarsu na kusan rabin sa’a kafin daga bisani su bar wajen. Sojojin sun yi iya kokarinsu wajen ganin sun kare motocin amma ana zargin cewa an umarce su da su bar wurin.” Shugaban ‘yan fashin, Bello Turji, da ‘yaransa, wadanda adadinsu ya kai 30, sun fito ne a cikin wani faifan bidiyo da ya yadu a kafafen sada zumunta na yanar gizo, inda ya ce sun kwace motoci daga hannun sojoji. An ga ‘yan bindigar a cikin faifan bidiyon suna kwashe akwatuna biyu da ake zargin akwai harsasai da wasu kayayyaki daga cikin motar da aka bari.
|
96
|
<|title|>Garkuwa da mutane: Likitoci sun janye yajin aikin gargadi na kwanaki 7
<|section|>news
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki a yau Litinin bayan yajin aikin gargadi na kwanaki 7 da suka yi bisa garkuwa da mambar su, Dakta Ganiyat Popoola. An yi garkuwa da Popoola ne watanni 8 da su ka gabata kuma har yanzu ba a sako ta ba. Koda ya ke, kungiyar ta ce zata sake yin duba kan kokarin gwamnatin tarayya na magance bukatar ta ta cikin makwanni 3. A ranar Litinin din da ta gabata ne dai likitocin suka fara yajin aikin na gargadi domin matsawa don ganin an kubutar da likitar wacce ke kula da cibiyar kula da lafiyar ido ta Kaduna. An sace ta da mijinta a ranar 27 ga watan Disamba na 2023. Yayin da aka saki mijinta a watan Maris, Popoopla da dan uwanta sun kasance a hannun masu garkuwa da mutane. Gwamnatin tarayya dai a ranar Alhamis ta ce zata dabbaka tsarin ‘Ba aiki ba biya’ ga likitocin. Sai dai likitocin sun ce baza a yi musu barazana da hakan ba. Da ya ke zantawa da jaridar Punch, shugaban kungiyar likitocin na kasa, Dakta Dele Abdullahi ya ce ” mun dakatar da yajin aikin a yanzu. Zamu gana domin ganin ci gaban da aka samu daga gwamnati nan da makwanni 3.”
|
97
|
<|title|>Ziyarar Tinubu zuwa China za ta haɓaɓaka hulɗar kasuwanci da aikin yi a Nijeriya — Jakadiya
<|section|>news
Yan Yuqing, karamar jakadiyar kasar China dake Legas, ta ce tana kyautata zaton ziyarar shugaba Bola Ahmed Tinubu a kasarta za ta bunkasa hulɗar kasuwanci da samar da ayyukan yi a Najeriya. Madam Yuqing ta shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Kasa a Legas cewa hakan zai kara habaka tunanin samun riba, farin ciki, da tsaron mutanen kasashen biyu. “Muna fatan mu dauki taron koli na Beijing da ziyarar Shugaba Tinubu a matsayin wata dama ta zurfafa hadin gwiwa a tsakanin kasashenmu a fannonin masana’antu, aikin gona, gina kayayyakin more rayuwa, samar da kudade, rage talauci, fasahohin zamani, da sauransu.” NAN ta ruwaito cewa, taron koli na dandalin tattaunawar hadin gwiwar China da Afirka don , FOCAC, zai gudana ne daga ranar 4 zuwa 6 ga watan Satumba, a nan birnin Beijing, mai taken “Hada Hannu don Ci Gaba da Zamanantar wa da Gina Al’ummar Sin da Afirka tare da Makomar Mai Inganci” Madam Yuqing ta ce taron zai yi amfani da takardun sakamako guda biyu, sanarwar da shirin aiwatarwa don samar da babban ra’ayi a tsakanin bangarorin biyu, da tsara hanyar aiwatar da hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka cikin shekaru uku masu zuwa. Ta ce, shugaban kasar China , Xi Jinping, da Tinubu, za su yi nazari kan yadda za a yi hadin gwiwa tare da tabbatar da ajendar “Sabon Fata” ta shugaba Tinubu.
|
98
|
<|title|>YANZU-YANZU: Shahararren mawakin siyasar nan, Garba Gashuwa ya rasu a Kano
<|section|>news
Allah Ya yi wa shahararren mawakin siyasar nan, Alhaji Garba Gashuwa rasuwa. Ƴar marigayin ta shaida wa wakilin DAILY NIGERIAN HAUSA cewa mahaifin na su ya rasu yau da asuba a Asibitin Kwararru na Murtala da ke Kano. Ta ce ya rasu bayan ya sha fama da jiyya. A cewar ta, marigayi Gashuwa ya haura shekara 70 kafin rasuwar ta sa. Ya rasu ya bar ƴaƴa 11, mata biyu da kums jikoki da dama. Gashuwa ya shahara wajen yi wa masu mulki wakoki tun lokacin mulkin soja har zuwa na farar hula. Mafi shahara a wakokin sa ita ce wacce ya yi wa shugaban ƙasa na soja a wancan lokacin, Janar Ibrahim Badamasi Babangida. Sannan ya yi wa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari waka da kuma jam’iyyar sa ta ANPP lokacin yana yakin neman zabe a 2023. Daily Nigerian Hausa na addu’ar Allah Ya gafarta masa, Ya kuma kyautata bayan sa.
|
99
|
<|title|>Tuntuni Tinubu ya gano cewa Buhari ba ya yin shi a zaɓen 2023 — Sule Lamido
<|section|>news
Sule Lamido, tsohon gwamnan jihar Jigawa, ya bayyana cewa tun da fari , shugaban kasa Bola Tinubu ya gane cewa tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ba ya yin shi. Lamido, jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, ya bayyana haka a wata hira da jaridar Nigerian Tribune. Ya ce: “Kafin babban taron jam’iyya na ƙasa, Tinubu, a garin Abeokuta na jihar Ogun, ya bugi kirji da cewa lokaci ya yi da zai mulki Najeriya, shi kuma Buhari yana kallo. Bai taba son Tinubu ba. Akwai wanda yake so. “Bai aminta da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ba ma; Ahmed Lawan ya ke so, amma lissafinsa bai yi ba. Kun jagoranci Arewa shekara takwas, kuna son wani dan Arewa ya kara shekaru takwas?! A’a, watakila daga baya amma akwai wasu abubuwan da ba za ku iya canza ssu ba, ba a Najeriya ta yau ba. “Shugaban Najeriya, bayan ya shafe shekaru takwas yana mulki, bai da karfin gwiwa wajen tsayawa kan zabin da ya yi. Yana can wajen taron kuma Tinubu wanda bai taba so ba, bai taba yarda ya fito ba. Tinubu ya san cewa nasararsa ba daga Buhari ba ce, don haka Buhari bai tsinana masa komai ba,” in ji Lamido.
|
End of preview. Expand
in Data Studio
asali-x Dataset
A cleaned and curated corpus of Hausa-language news articles from 2020-2025. This dataset is designed for training and fine-tuning language models for Hausa text generation and understanding tasks.
Dataset Structure
The dataset is split into training and validation sets:
- Training set: ~57K articles
- Validation set: ~3K articles
Fields
- text: Article content in the format
<|title|>... <|section|>... body - id: Unique integer identifier for each article
Quality Checks
The dataset has been processed with the following quality measures:
- Duplicate removal (based on MD5 hashing)
- Short article filtering (articles under 200 characters are flagged)
- Unique ID verification
Usage
from datasets import load_dataset
# Load the dataset
dataset = load_dataset("superfunguy/asali-x-news-hausa", "text_only")
# Access training and validation splits
train_data = dataset["train"]
val_data = dataset["validation"]
Data Collection
The dataset was generated by aggregating news articles from three primary Hausa-language news platforms:
- Daily Nigeria Hausa
- Aminiya (Daily Trust Hausa)
- Legit Hausa
License
This dataset is released under the Creative Commons Attribution 4.0 International License (CC-BY-4.0).
Citation
If you use this dataset in your research, please cite:
@misc{asali-x,
author = {superfunguy},
title = {asali-x Dataset},
year = {2024},
publisher = {Hugging Face},
journal = {Hugging Face Hub},
howpublished = {\url{https://huggingface.co/datasets/superfunguy/asali-x-news-hausa}}
}
- Downloads last month
- 66